6 Faburairu 2016 - 10:49
Al-qaeda Ta Dauki Alhakin Sace Turawan Australia 2 A Burkina Faso

Kungiyan yan ta'adda ta Al-qaeda ta bada sanarwan cewa ita ce ta dauki nauyin sace turawan Astralia biyu a kasar Borkina faso.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a jiya jumma'a ne kungiyar yan ta'adda ta almurabidun wacce take biyayya ga kungiyar Al-qaeda ta aike da wani sauti a yanar gizo inda ta dauki nauyin sace turawan Australian a cikin watan Jenerun da ya gabata, kuma a shirye take ta yi musayar daya daga cikinsu da wata mata da ake tsare da ita a kasar ta Borkina faso.

A ranar 17 ga watan jenerun da ya gabata ne gwamnatin kasar Australia ta bada sanarwan cewa yan kasarta biyu sun bace a kasar Borkina faso bayan wani harin da yan ta'adda suka kai kan wani hotel a birnin, harin da ya halaka mutane 30 mafi yawa yan kasashen waje.288