Babban Hafsan sojin na Nijar Janar Seini Garba ya bayyana hakan ne a jiya Talata inda ya bayyana cewar: kasar Nijar ta aikata abubuwa masu yawa a bangaren fada da kungiyar ta Boko Haram, lamarin da ya sanya ta samun nasarori masu girman gaske a wannan fada da take yi. Don haka babban hafsan hafsoshin ya sha alwashin cewa nan ba da jimawa ba za su murkushe kungiyar ta Boko Haram a kasar.
A baya ma dai mutanen yankunan da annobar Boko Haram din ya fi shafa a Jamhuriyar ta Nijar musamman yankin Diffa, inda Boko Haram din suka fi addabarsu sun bayyana gamsuwa da jin dadinsu dangane da yadda ake ci gaba da samun zaman lafiya a yankin sakamakon fatattakar 'yan Boko Haram din da sojojin na Nijar suka yi.
Kasar Nijar dai tana daga cikin kasashen Yammacin Afirka da suka hada da Nijeriya, Kamaru, Chad da Benin da suka kafa hadaka don fada da 'yan kungiyar Boko Haram din da suka zamanto musu ala kakai.288