Kabore wanda tsohon Firaminista ne a kasar ya lashe zaben shugaban kasar ne da kuri’u kashi 54.49, yayin da Zaphirin Diabre ya zo a matsayi na biyu da yawan kuri’u kashi 29.65.
Zaben Burkina Faso dai ya kankama ne ba tare da wani tashin hankali ba, duk da an shafe shekara guda kasar na cikin rudanin siyasa, bayan kawo karshen mulkin Blaise Compaore