22 Nuwamba 2015 - 10:37
Gwamnati ta gargadi  masu kokarin  kafa kasar Biafara

A Najeria Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya ce gwmanati ba za ta sa ido wasu na ci gaba da furta kalaman ballewar wani yanki daga cikin kasar ba.

Bayanen  wadanda ake kallo a matsayin gargadi ga masu kokarin kafa kasar Biafara, mataimakin shugaban kasar ya furta su ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin bikin yaye dalibai a cibiyar bayar da hora da samar dubaru da ke Kuru kusa da Jos.

Osinbajo ya ce Najeriya dai kasa ce da ke kan turbar dimokuradiyya, kuma dole a bi hanyoyi irin na dimokuradiyya wajen gabatar da wata bukata amma ba ta hanyar tayar da hankula ba.288