Yayin da kasashen duniya suka yi Allah wadai da hakan, shugaban Amurka Barack Obama, wanda yanzu haka ke halartar taron shugabannin kasashen yankin Asiya da Pasifik, ya yi kakkausar suka a game da wannan hari da aka kai a Bamako.
Shi ma dai bababban magatakarda na MDD Ban Ki-moon, ya ce ya damu matukar a game da halin da kasar ta Mali ta fada a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin taimaka wa Mali domin komawa kan turbar dimokuradiyya.288