Kwamandan dakarun kare Musulunci na Kasar Iran Janaral Hussain Salami ya bayyana cewa za Su yanke hannu duk wanda ya yi gigin kawo wa Iran Hari.
Ganaral Hussaini Salami Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya fadi hakan ne a yau Alhamis a wajen bukin rufe Atisayan soji da dakarun kare juyin suka gudanar na gwada wasu sabbin makamai da suka kera dama dakaru dubu hamsin saka halarta, inda ya kara da cewa Hakuri da tsayin daka da koyi da karantarwa Ashura da alummar Iran suka yi ne ya basu damar tarwasta makircin makiya da hakan ya tilasta musu komawa bangaren Diplomasiya mai makon ci gaba da barazanar kai harin soji kan Iran.
Har ila yau kwamandan ya nuna cewa magoya baya da masu adawa da yarjejeniyar da aka cimma da kasashen turai kan shirin Iran nan nukiliya na zaman lafiya a Amurka dukkansa makiya Alummar Iran ne, kuma ana amfanin da su ne a matsayin makami wajen cutar da kasar Iran, don haka dakarun kare juyi a shirye suke kuma suna lura da duk wani motsin da makiya suke yi, kuma suna jiran dama ne so kona dukkan manufofin siyasa dana tattalin arzikinsu matukar suka yi gigin kaiwa Iran Hari288.