30 Agusta 2015 - 17:49

kwanaki biyu ke nan alummar kasar malesiya suna gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin pira Ministan kasar sakamakon zargin da ake masa da hannu a sama da fadi da wasu makuden kudade wannan matakin ya biyo bayan wani rahoto da wata mujallar ta buga da aciki ake zargin pira ministan kasar da hannu wajen bacewar kudi har Euro miliyan 640.

A Malesiya yau kwanan na biyu da ake gudanarda zanga-zanga kin jinin firaministan kasar Najib Razak bisa zarginsa da hannu a wata babbar badakallar karkata akalan wasu kudaden kasar.

Dubun dubatar al’ummar kasar ne suka sake komawa zanga-zanga a yau bayan shafe daren jiyya suna zamen durshin.

Kawo yanzu dai babu wani cikas a zanga-zangar dake gudana duk kuwa da cewa ‘yan sanda kasar sun haramta ta.

Kiraye-kirayen kin jinin Najib Razak dai sun biyo bayan da mujallar Wall Street Journal ta bankado a watan Yuli daya gabata labarin cewa masu bincike a kasar Malasiya sun gano cewa an zubawa firaministan kudade a asusun sa da yawan su kai milliyan 640 na EurO.288