28 Agusta 2015 - 15:20

Wanda ya jagorancin sallar juma'a a birnin tehran ya yi gargadi game da kokarin da makiya suke yi na neman tsoma baki a fagen siyasar kasar Iran bayan cimma yarjejeniyar nukiliya, su makaiya suna haifar da fitintinun a kasashen duniya duk da sunan musulunci tare da bayyana shi a matsayin Addinin mara tausayi da sananin ya kamata hatta yara da manya ma basu tsira ba, ya kara da cewa a zahiri ana ya ki da kungiyar ISIS ne amma hakikanin gaskiya da Amurka da Isra'ila da Birtaniya ne da suke basu makami da dukkan taimakon da suke bukata.

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau a birnin Tehran ya yi gargadi game da makircin makiya na neman bakin fada aji a fagen siyasar kasar Iran.

Hujjatul Islam Kazim Siddiqi wanda ya jagorancin sallar Juma’a a babban masallacin juma’ar birnin Tehran ya bayyana acikin hudubarsa cewa wadanda ake tattaunawa da su kan batu nukiliyar Iran sun yi kokari ne wajen ganin sun tsawaita lokacin tattaunawar amma yin taka tsantsan da sanya hikima da kuma matsayin da jagora mai hangen nesa ya dauka ya sa aka kai irin wannan matsayin, duk da haka makiya sun dauka cewa za su iya amfani da cimma matsaya kan yarjejeniya wajen yi tasiri a harkokin siyasar kasar kamar yadda suka yi kokarin yi a lokacin fitinar shekara ta 88 da ta gabata amma dai hakarsu bata cimma ruwa ba.

Da ya karkata game da batun ta’addanci kuwa limamin ya nuna cewa makiya suna haifar da fitina a kasashen duniya ta hanyar fakewa da sunan musulunci tare da bayyana shi a matsayin addanin da bashi da tausayi da yin amfani da hankali balle kunya, kuma ba wai ba ya kula da hakkokin sauran yan uwansa ba ne kawai hatta manya da yara kanana basu tsira ba. A zahiri muna kalubalnatar kungiyar ISIS ne amma asalin wadanda suka kirkirota kuma suke basu kariya su ne kasashen Amurka da ISra’ila da birtaniya kuma sune ake tunkara288.