Yara kanana da Mata na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su a Shar Shaheed gabacin birnin Kabul. Kuma harin ya lalata gidaje da dama.
Hukumar ‘Yan Sandan Afghanistan tace kimanin mutane 128 suka samu rauni, kuma ana ci gaba da tsakulo wadanda gini ya rubta da su sakamkon harin.
Zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin, wanda ke zuwa a yayin da aka samu sauyin shugabanci a kungiyar Taliban.288