18 Yuli 2015 - 16:50
Mutane da dama ne suka jikkata a hadarin jirgin kasan Africa ta Kudu

Fiye da mutane 200 ne suka sami raunuka a hadarin jirgin kasa, da ya auku a kudancin birnin Johannesburg na kasar Africa ta Kudu. Masu aikin ceto da jami’an kula da lafiya sun fidda wadannan alkaluman ne a lokacin da jami’an gwamnati ke gudanar da bincike a wurin da hadarin ya faru.

Sai dai ba a sami rahoton mutuwa ba, a hadarin da ya faru sakamakon wani jirgin kasar da ke tafiya, da ya afka wa wani jirgin dake tsaye.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ake samun dandazon jama’a dake kokarin komawa gidajensu, bayan tashi daga wajen aiki a tsakiyar birnin na Johannesburg.
Mai magana da yawun hukumar jiragen kasa ta Africa ta Kudu, yace har yanzu ba a gano musabbabin hadarin ba, sai dai a cewar shi suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.288