13 Mayu 2025 - 20:16
Source: ABNA24
Ganawar Musamman Ta Ayatullah Jawadi Amoli Tare Da Ayatullah Sistani A Najaf Ashraf

Bayar da Kyautar tafsirin kur'ani Mujalladai 80 mai suna (Tasnim) a ganawar da manyan maraja'ai biyu suka yi.

Ayatullahi Jawadi Amoli ya gana kuma ya tattauna da Ayatullah Sayyid Ali Sistani a ziyarar da ya kai kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (A.S.) - ABNA - ya ruwaito maku cewa: A ci gaba da ziyarar da Ayatullahi Jawadi Amoli ya kai kasar Iraki a fannin ilimi, ya gana da Ayatullahi Sayyid Ali Sistani a lokacin da yake birnin Najaf mai tsarki. Taron ganawae wanda ya gudana cikin yanayi na kud da kud da ruhiyya, ya gudana ne domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi addini, al'adu da zamantakewa na duniyar musulmi.

A cikin wannan ganawar, Ayatullahi Jawadi Amoli ya yaba da matsayin Ayatullah Sistani na ilimi da ruhiyya da irin rawar da yake takawa wajen kare hadin kan al'ummar musulmi da shiryar da al'ummar Shi'a. Har ila yau Ayatullahi Sistani ya bayyana gamsuwarsa da wannan ganawar da kuma jin dadin hidimar ilimi da tafsiri na Ayatullah Jawadi Amoli.

A yayin wannan ganawar, Ayatullahi Jawadi Amoli ya gabatar da cikakken littafin na tafsirinsa mai daraja mai suna "Tasnim" mai kunshe da mujalladi 80 ga Ayatullahi Sistani kuma da kansa ya gabatar da mujalladai 80 ga marji'in mai alfarma. Ayatullahi Sistani ma ya karbi wannan littafin mai alfarma na ilimi tare da girmamawa ta musamman tare da nuna farin cikin wannan kokari na shekaru arba'in.

Ayatullahi Sistani ya yaba da wannan aiki mai dorewa, sannan ya dauki Tasnim a matsayin abin alfahari ga 'yan Shi'a, sannan ya jaddada matsayin kur'ani a cikin ilimin addini yana mai cewa: Wajibi ne a bjirar da ruwayoyin Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) zuwa ga Alkur'ani kuma kawai za'a iya dogara da su ne idan sun yi daidai da Alkur'ani.

Ya ci gaba da jaddada hadin kan Hauzozi na Shi'a na duniya inda ya ce: Mahangar mu game da makarantar Qum ba ta da bambanci da namu na makarantar Najaf, kuma za mu yi hidimar dukkan makarantun biyu gwargwadon iyawarmu.

Haka nan kuma ya yi ishara da masaniyar da ya yi ta baya da ayyuka da dabi'un ilimi na Ayatullah Jawadi Amoli ya kara da cewa: Mun ji labari da yawa game da kai da ayyukanka na ilimi, amma gani ya kori ji!

A wani bangare na wannan ganawar, Ayatullahi Javadi Amoli ya yaba da matsayin Ayatullah Sistani inda ya ce: Kai kamar uba ne mai tausayi da tausayawa ga 'yan Shi'a da al'ummar Iraki; Kasancewar ku babbar ni'ima ce ga duniyar Musulunci.

Haka nan kuma ya bayyana irin rawar da marji'in takawa wajen kiyaye tsarin zamantakewar Iraki da tunkarar kungiyoyin takfiriyya a matsayin mai tarihi da dawwama, sannan ya kara da cewa: Makarantar Najaf kai tsaye ko ta fakaice ta kasance wata babbar fa'ida ga al'ummar musulmi.

An yi marhabin da wannan taron ganawar tare da samun kulawa daga kafafen yada labarai da na makarantun hauza, kuma an bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na hadin kan kimiyya da hadin kan marja'o'in addini.

Your Comment

You are replying to: .
captcha