Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta bisa nakaltowa daga Al-Mayadeen cewa, a ci gaba da hare-haren wuce gona da irin da Amurka ke kaiwa kasar Yemen, jiragen yakin kasar sun kai wasu jerin hare-hare a wasu garuruwan kasar ta Yemen a safiyar yau litinin, lamarin da ya yi sanadiyar shahada da jikkata wasu fararen hula.
Wakilin Al-Mayadeen ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin Amurka sun sake kai hari a yankin Al-Juba da ke lardin Marib sau biyu a jere. Haka nan yankin Harf Sufyan da ke lardin Amran ya fuskanci hare-haren na Amurka har sau uku, sannan kuma an kai hari a yankin Jabal al-Mahurit da ke lardin al-Mahurit da ke yammacin Sanaa sau daya.
Kamfanin dillancin labaran Saba na kasar Yemen shima ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin Amurka sun kai hari a yankin Sirwah da ke lardin Marib har sau hudu.
An kuma bayar da rahoton hare-hare biyar da jiragen yakin Amurka suka kai a lardin Saada da ke arewacin kasar Yemen.
A cikin wadannan hare-haren, jiragen yaƙin na Amurka sun kai hari kan ababen more rayuwa na fararen hula na kasar Yemen, da suka hada da muhallan kiwon lafiya da tsafta a yankin Asr da babbar kasuwar jama'a da unguwar Faruah al-Shaabi da ke yankin Shu'ub, lamarin da ya janyo hasarar kudi ga gidaje da shaguna na 'yan kasar ta Yemen.
Ma'aikatar lafiya ta kasar Yemen a birnin San'a ta sanar da cewa, an kashe 'yan kasar Yemen 12, yayin da wasu 30 suka jikkata sakamakon harin da Amurka ta kai kan kasuwar Al-Farwa Al-Shaabi da unguwarsu, kuma da alama adadin ya karu.
Hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen ya kara tsananta ne bayan da gwamnatin Isra'ila ta sake mamaye yankin Zirin Gaza tare da ci gaba da kai hare-hare a yankin. Dakarun kasar Yemen sun sake dawo da shingensu da hare-harensu na sojojin ruwa na gwamnatin kasar suka yi a tekun Bahar Maliya da kuma tekun Larabawa tare da kai farmaki kan jiragen ruwan Isra'ila domin nuna goyon bayan Gaza da kuma kare al'ummar Palastinu.
Your Comment