18 Afirilu 2025 - 14:05
Source: Irna
Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Amurka A Yaman

Bayan harin da jiragen yakin Amurka suka kai kan tashar man fetur ta Ra'as Isa da ke lardin Hudaidah na kasar Yaman, wanda ya yi sanadin shahadar ma'aikata da fararen hula da dama, kungiyoyin gwagwarmaya na Palasdinawa sun yi kakkausar suka ga wannan mummunan hari.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya habarta bisa nakaltowa daga shafin yada labaran Falasdinu cewa, kungiyar gwagwarmayar 'yantar da Falasdinu ta bayyana harin da Amurka ta kai a daren Alhamis kan Ra'as Isa a matsayin wani laifin hari da ya kunshi nau'ukan yaki, tare da sanar da cewa jiragen yakin Amurka sun sake kai hare-hare a yankin bayan an fara kai agaji da kashe gobara.

Wannan kungiyar ta jaddada alakar da ke tsakanin laifuffukan da Amurka ke yi da gwamnatin sahyoniyawan a yankin, inda ta bayyana cewa: Makiya dai duk daya ne.

Kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana matakin da cewa "aiki ne na wuce gona da iri da kuma bayyanannen misali na laifin yaki," tare da tantance shi a matsayin goyon bayan kisan kiyashi da ake yi wa al'ummar Palasdinu. Har ila yau kungiyar ta yi kakkausar suka kan matakin da hukumar samar da abinci ta duniya ta dauka na dakatar da tallafin abinci ga yankunan da aka kai hari a kasar Yemen.

Harkar Mujahiddin Falasdinu, ta bayyana cikakken goyon bayanta ga al'ummar kasar Yemen, ta dauki harin da aka kai tashar jiragen ruwa ta Ra'as Isa a matsayin ci gaba da laifukan gwamnatin sahyoniyawan a Palastinu tare da jaddada cewa, Amurka da kawayenta ba za su taba samun karya ikon azamar al'ummar Yemen ko gwagwarmayar al'ummar musulmi ba.

A cewar IRNA, jiragen yakin Amurka sun kai hari a yankin Ra'as Isa sau hudu a daren jiya Alhamis, ciki har da tashar mai na Ra'as Isa da ke lardin Hudaidah na kasar Yemen.

Ofishin ma'aikatar lafiya ta kasar Yemen a lardin Hudaidah ta sanar da cewa, an kashe fararen hula 38 tare da jikkata wasu 102 a wadannan hare-haren.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar da cewa, sakamakon tsananin hare-haren da ake kaiwa ta sama ana samun karuwar shahidai da jikkata sakamakon wannan aika-aika.

Your Comment

You are replying to: .
captcha