7 Afirilu 2025 - 22:00
Source: ABNA24
Munasabobin Da Suka Faru A Cikin Watan Shawwal Daga Rana Farko Zuwa Ranar 17 Ga Wata

Daga cikin muhimman munasabobin musulunci da suka faru a watan Shawwal akwai manyan yakokin musulunci kamar yakokin Uhudu sa Khandaq da Hunain da kuma rushe makabartar Baqi’a da ke madina da Wahabiyawa suka yi da kuma wafatin Imamul Bukari shugaban masu ruwaito hadisan Ahlus-Sunnah Wal’jama’a

1/Shawwal/256H

Wafatin Imamul Bukhari Rh Shugaban Masu Ruwaito Hadisai

                Ranar 1 ga watan Shawwal Ita ce ranar idin karamar salla mai albarka, kuma yini ne da yake farantawa muminai rai yayin kammala azuminsu da yin biyayya ga umarnin Ubangijinsu, kuma zuciyar muminin a wannan rana ta kasance a rataye tsakanin tsoro da fata saboda bai sani ba ko an karɓi azuminsa ya kasance cikin mutane masu farin ciki da annashuwa, ko kuwa ayyukansa, azumi basu karbu ba kaga zai kasance yana daga Masu baƙin ciki, Musulmi ya kamata ya yawaita addu’a da rokon Allah ya saka masa da alheri ya kuma yarda da shi ya karbar azuminsa da ibadarsa.

                A irin daren wannan rana ne dai Imamul Bukhari yayi Wafati wanda ya dace da daren asabar bayan Sallar isha kuma an masa Sallar washegarin ranar wato ranar idi kenan a shekara ta 256h ya rasu yana dan shekara 62 a duniya.

                Imam Muhammadul Bukhari kamar yadda yake sanannen abu ne shi babban malamin hadisi ne kuma marubucin Littafi mafi girma na hadisi a wajen Ahlussunna Wal’jamah wato Sahihul Bukari an Haifeshi a daren Jumaah 13 ga watan shawwal shekara ta 194h a Birnin Bukhara dake Lardin Kurasan. amma asalinsa dan Garin Balkh ne dake daya daga cikin kananan hukumomi dake Afganistan ta yanzu. Imam Bukhari yayi fice tun yana dan karami bisa abokan karatun zamanin sa wanda ya dukufa wajen neman Ilimi tun yana karami bayan wafatin mahaifinsa inda ya hardace Alkur’ani tun yana dan shekara 10 kuma ya shahara wajen kaifin basira da Hadda wanda tun yana karami ya haddace hadisai dubu sabain tun yana karami yasamu matsalar Ido inda daga baya Allah ya dawo masa da ganinsa.

                Inda abokan karatunsa ko wane lokaci kamar yadda suka saba suna zuwa daukar karatu wajen malamai yakasance baya rubutu kamar yadda abokansa sukeyi har a wata rana abokan karatun sa suka dame shi me ya sa baya rubutu baya zuwa tare dasu sunayin bitar abinda suka karanta sai yace kun dame ni dayawa ku kawo duka abunda kuka rubuta in biya maku haka suka bude shi kuma yana fadi batare da yana kallon abinda ke garesu ba, su kuma suna ta gyara abinda sukai kuskuren rubuta shi daga abinda sukaji daga gareshi .

                Ya kasance yasamu tarbiya mai kyau yanada halaye na daraja inda ya mai da hankali wajen neman Ilimi musamman na hadisi, tun yana dan shekara 18 ya yaje hajji inda ya zauna a Makka yana me neman hadisi aciki sanna yayi tafiye tafiye zuwa sauran malamai daya karbi hadisi daga wajen su a garuruwa da dama inda yakarbi hadisi daga wajen malamai sama da dubu yakasance yakan tashi cikin dare kusan sau 20 yana mai rubuta abinda yazo  masa cikin tunanin sa.

                Imam Bukhari lokacin da yake bada darasi saboda yawan masu karbar hadisi yana da masu amsa maganarsa idan yayi na karatu guda 70 domin isar da ita ga wanda suke nesa a wajen taron karatun kowanne yana maimaita abinda yafada don kowa yaji.

                Yanayin Rayuwa yabawa Imamul Bukhari dama wajen yin rubututtuka da dama don bada gudunmawarsa ga Addinin Allah, Allah ya ba shi kaifin basira, haƙuri cikin ilimi da jajircewa don cimma shi,ya tattara cikakken ilimin hadisin Annabi da yanayin mazajensa da suka ruwaice , Al-Bukhari ya ce ya fara rubuta littafa tun yana matashi yana dan shekara goma sha takwas. Kuma ya rubata sama Littafa 20 wanda mafi shahransu shine Littafin Sahihi Bukari.

Allah Ta’ala Yayi Masa Rahama.

Rana Ta 8 Ga Shauwwal  1344h

A irin wannan Rana ne Wahabiyawa yan ina da Kisa suka Rushe kaburburan A’imma asa dake makabartar Bakial garkad atre da kabarain Sayyidan Hamza As da suaran kaburbutran Shahidai.

Kamar yadda yake sannan abu ne ba ba wannan karo na farko da sukayi irin wannan mummuna aikin ba musamman anan makarabartar na farkon sunyi a shekarata 1220h sunyi hakan domin fito da kiyayyarsu da gabarsu fili ga Annabin rahama da Iyalansa As wanda wannan aikin dama sun gajeshin tun daga manyan su Abu Sufyan da sauran wadan da suka biyo bayansu kamar su kalaifana abbasawa Mutawakkil wanda ya rushe kabarain Imam Husain As Ba sau daya ba kuma yahana zuwa ziyarar ta hanayr yanke Hannun duk wanda yaje.

Kamar yadda yake sannan abu ne akwai Aimmah guda hudu a wannan makabarta  sune Imam Hasan As Imam Sajjad ALiyu Zainul Abideen As Imam Muhammadul Bakir AS Imam Ja’afarus Sadik As kamar yadda Makabartar take dauke da Kaburburan daya daga cikin Mata Yaya  na Annabi As da Matan wanda suka shayar da kamar su Sayyidah Halimatussaadiyyah da Sayyidah Fatimah Bintu Asad Mahfiyar Imam Ali As.

Dukkan wadannan rushe-rushen kabarin hukumaar Saudiya cxe ke nauyin AIkatasu bayan malamanta sun bada fatawar rushe su.

8/Shawwal Shekara ta 8h

A irin wannan rana ne dai yakin Hunain ya auku tsakanin Mu’muinai da Mushirkan Kabilolin hawazin da bani Hilal da Nasr Jashmi wanda malik dan Auf yake jagoranta a wani kwarin ruwa da ake kira Hunain tsakanin maka da Daif.

Yakin ya faru bayan bude maka da kwana 13 bisa wata ruwaya

Wanda wannan yakin bisa Jagorantar Annabin Rahama Sawa ne inda adadin Musulmai yakai dubu 12 ammam bayan fara yakin inda mushrikai sukayiwa musulamai tarko ta hanyar mammayarsu da fara yi masu rowan kibau inda wanda suke gaban rundunar mu musulmai suka watse har takai ba wanda yayi saura acikin su sai mutum goma tara daga cikin banu hashin ne daya daya kuma mutumin madina. Inda bayan musulmai sunga dake war Annabin da wanda suke tare dashi da kuma kiransu da yayi suka fara dawoiwa tare da tabbatuwa suna tattaruwa.

Kamar yadda batun wannan yakin yazo acikin Alkur’ani mai girma inda yake nuna taimakon Allah Taalaa ga Musululmai bayan sunyi tinkaho da yawan da suke dad a kuma mamayar da akai masu inda suka tarwatse sauran wanda sukayi saura daga cikin Banu Hashin sukai wa Annabin rahama Runfa da Jikkuna su da garkuwowin su inda A lokacin Imam Ali shi kadai ya tunkari wadannan Mushrikai har Allah Taala ya saukar da Nutsurwa ga Annabinsa da Mu’uminai ya saukar da Rundunoni na Mala’iku ya yaki Mushirikai dasu.

15/Shawwal/3

Yakin Uhudu Da Shahadar Sayyaduna Hamza As

                A irin wannan rana ta 15 ga watan Shawwal ne a shekara ta uku bayan hijira ne dai yakin Uhud ya Auku tsakanin Mu’uminai bisa jagorancin Annabi Muhammad Sawa da Mushrikan Larabawan Makka akusa da dutsen Uhud da zimmar daukar fansar Yakin Badar da ya wakana kusan shekara daya data gabata.

                Bayan mushrikai sun sha kayi a yakin Badar sun fara shirin daukar fansa ta hanyar yin shirin yaki bisa shugabancin Abu Sufyan. Wanda ya kasance Annabi da sauran Muhajirai sun so ayi yakin a cikin Madina ne, amma wasu Sahabbai wanda suka hada da Sayyidana Hamza As sun so ayi a wajen madina ne wanda daga karshe Annabi Sawa yayi azama suka fita daga cikin birnin Madina yakin ya kaure wanda a  farkon yakin Mu’uminai sunyi nasara akan Mushrikai har sun korasu.                 Amma daga bisani sai wasu gungu na Sahabbai masu kibau bisa jagorancin Abdullahi dan Jubair da Annabi ya sanya su tsaron bayan Rundunar Mu’uminai suka gangaro don gani cewa mu’uminai sunyi nasara duk da Annabi Sawa yace masu karsu motsa daga gurin da suke komai zai faru, inda saukowar su ya sanya Mushirikai bisa Jagorancin Khalid Bin Walid suka yiwa Rundunar Mu’uminai qawa suka zagaye su ta baya inda hakan yasa mu’uminai suka tarwatse tare da guduwa. Babu wanda yayi saura tare da Annabi Sawa sai dai yan mutane kadan na farkon su shine Imam Ali As inda yayi ta kore Rundunar Mushrikar daga wajen Manzon Allah Sawa wanda a wannan yakin An jima Annabin rahama ciwo a goshi tare da karyewar hakuransa guda biyu nagaba.

                Kuma a wannan yakin ne Sayyiduna Hamza Yayi Shahada inda bawan Hindu bisa umarninta ya soke shi da mashi. Inda adadin wadanda sukai shahada daga mumunai yakai 70 kuma manzon Allah Sawa yayi salla ga kowane daya daga cikin su shi kadai kuma a kowace sallah yana sanya gawar Sayyiduna Hamza As a kusa da kowani gawa da zai wa sallah kunga kenan shi Sayyiduna Hamza As Annabi Sawa ya masa salla sau 70 da wani abu kenan wanda gaba dayan su anbinne su ne akusa da wannan Dutsen na Uhud kamar yadda sunayen su yazo a Littafan tarihi. Suma mushirikai an kashe masu adadin daya kai sama da 20

                Bayan yakin Uhud Sayyidah Fatimah As ta samu labarin abun yafaru a yakin da kuma jiwa manzon Allah ciwo da akayi saita yunkura ta tafi fagen yakin tare da wasu gungu na mata inda suka dauki ruwa da kayan abinci suka tafi da shi inda suka bawa wadanda da suka ji ciwo ruwa suka sha tare da daure guraren da suka ji ciwon inda Sayyidah Fatimah As da kanta ta kula da mahaifinta tare da wanke masa fuskarsa inda ta kona guttun tabarma ta sanya tokar a jikin ciwon don jinin ya dena zuwa.

 Kamar yadda Alkur’ani yayi nuni da faruwar wannan yakin acikin surar Al’Imran daga ayata 121 zuwa ta 171.

17/Shawwal/5h

                A irin wannan rana ne dai yakin Khandak ko Ahzab Kamar yadda suna biyu yazo acikin Alkur’ani ya faru kamar yadda muka sani yana daya daga cikin yakokin da Annabi sawa yayi a rayuwarsa shirin wannan yakin yafara ne bayan Haincin da kabilar Bani Nadir ne da sukai wa Manzon Rahama sawa inda yak ore daga wajen da suke a Madina su kuma sai sukai hadin gwiwa tare da Mushirkan Quraishawa da yan koransu don kawar da Musulunci da musulmai gaba daya.

Bayan shawaratar Mu’uminai da Annabi sawa yayi kan yadda za’a tunkarar wannan runduna akarshe Musulmai suka bi shawarar Babban Sahabin Annabi sawa Salmanul farisi na su gina gwalalo ko kwararo agefen Madina wanda wannan yakin musulmai sunyi nasara aciki inda tasa Mushrikai janyewa daga madina Manzon Allah Sawa yabar Ibn Ummu Maktum amtsayin magajinsa a Madina.

                wanda a wannan yakin ne Imam Ali As ya kasha Amru bin Abdul Wudd Al’amiry, wanda daidai yake da mayaka dubu shi kadai saboda jarumtar sa bayan fito na fito da yayi dashi, a wannan rana Annabin rahama yace dangane da wannan gwabzawa da Imam yayi da Amru (خرج الإسلام كله إلى الشرك كله) wato musulunci ya fito gaba dayan sa don tunkarar SHirka gaba dayan ta.

Inda adadin musulmai a wannan yakin dubu 3 adadin mushrikan kuraishawa da wanda sukai hadin gwiwa a wannan yakin yakai dubu 10.

Inda mushirikai suka killace tare da yiwa madina kofar raggo na tsawon kwana 15 a wannan kwanaki kawai anta musayar jefa kibiyoyin ne a wannan yakin musulmai shida ne suka yi shahada a bangaren Mushrikai kuma ankashe mutum 8.

Wanda labarin wannan yakin shima yazo a Alkur’ani mai girma ayata 214 suratul Bakara, ayata 55 suratun Nisa’I da kuma ayoyi suratul Ahzab ta zuwa ta 25 kamar yadda ita wannan surar ta samu suna saboda kawo kissar wannan yaki acikin ta.

Your Comment

You are replying to: .
captcha