6 Afirilu 2025 - 20:59
Source: ABNA24
Sheikh Ibrahim Alzakzaky {H}: Zuwa Yanzu Akwai Mutum 20 Da Akai Kashe A Hannun Jami'an Tsaro

Shaikh Zakzaky ya tambaya; "Me ya kawo masu gadin shugaban kasa kan titi suna harbi?"

Jiya Asabar 6 ga watan Shawwal 1446 (5/4/2025) Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da Wakilan bangarori daban-daban na Harka Islamiyya a Abuja.

A yayin ganawar Jagora (H) ya yi bayani dangane da Azumin Ramadan da aka kammala, da kuma bayyana manufar azumin a matsayin samun taƙawa.

Jagora (H) har ila yau, ya yi tsokaci dangane da yadda kafircin duniya, akan gaba Amurka da Haramtacciyar ƙasar Isra`ila ke ta'asa ga al'ummar Palasɗinawa a ƙoƙarinsu na shafe su daga doron ƙasa. Yace abin mamaki ƙasar Yemen ne kaɗai ƙasar Larabawa da take goyon bayan Palasɗi` nawa a hukumance da al'ummancensu. "In gwamnatocin ƙasashen Yamma suka zama suna marawa zaluntar Palasdinawa baya, to ku kuma kuma ƙasashen Larabawa meye naku na marawa kasashen Yamma baya?” 

Da yake magana akan ranar Quds Ta Duniya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana cewa an kwashe shekara 46 ana gudanar da ita duk shekara, tun 1979 da Imam Khomeini (QS) ya ayyanata. Yace, a duk duniya, har a fadar gwamnatin Amurka ana yin Muzaharar Quds a kammala lafiya, amma mu a nan ƙasar sai Allah Ya jarabce mu da wasu irin mutane da suke jin wai sunanmu wai Shi'a, mu ne muke goyon bayan Palasɗinu da Palasdinawa. “Yanzu mene ne ma'anar Shi'a a nan? Palasdinawan su ma Shi'a ne? Wanda ya san abin da yake yi ya duba su ta gani, muna iya cewa mu bamu san ma akwai Shi'a a cikinsu ba, in ma akwai ƙwarori ma ba ma tsammanin akwai ko masallaci daya na Shi'a, ko wani fitaccen Malami da za a ce na Shi'a ne a Palasdinu... To amma 'yan uwanmu ne Musulmi”.

Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda aka yi Muzaharar Quds din bana lafiya a birane da garuruwa kimanin 35 a Nijeriya, amma ba inda aka buɗe wuta sai a Abuja da wani mutum mai suna Nuhu Ribaɗo ya ƙudiri aniyar yin kisan kai.

Yace, "Da farko wani mutum mai suna Nuhu Ribaɗo ya rubuta takarda a ranar 26 ga watan Ramadan, - ana jibi za a yi Quds, cewa gashi nan 'yan Islamic movement, karkashin jagorancin Ibraheem Zakzaky, suna niyyar za su yi 'demonstrating' don nuna goyon baya ga al'ummar Palasɗinu, abin da suke kira ranar Quds Ta Duniya, za su yi a garuruwa kaza-kaza. To dama an san wadannan mutane da ta da hankali da kawo rikici, saboda haka ana gargadin dukkan sassan tsaro a dauki mataki mai tsauri don magance wadannan tarzoman da za su tayar”.

Shaikh Zakzaky ya cigaba da cewa: "To na san muna yi wannan Muzaharar Quds din tun Nuhu Ribaɗo yana Sakandire, tun bai taba sanin ma zai shiga Dan Sanda ba, tun yana yaro ƙarami muke yi, amma wai don rashin kunya wai shi ne ya san mu da tarzoma! Yanzu na san ko mahaukaci in kace masa, wadancan yan tarzoma ne. Zai ce maka karya ne".

Ya cigaba da cewa; "Dama mun san in muka ga rubutu irin wannan to shiri ne. Sukan ce sun bankado wani sirri, wadannan za su ta da tarzoma. To dama za su hada jami'an tsaro su je su bude wuta kenan, da nufin wai za su hana tarzoma ne.

“To sai kuma ofishin jakadancin Amurka da ke nan Abuja, shi ma sai ya fitar da takarda, cewa akwai ranar Quds Ta Duniya, wanda Islamic movement za su yi a nan Nijeriya, za su yi a garuruwa daban-daban, kuma za a yi a nan Abuja, amma ba a fadi a ina ne za a taso da Muzaharar ba, a ina za a kare, amma ana sa tsammani za a yi gumurzu tsakaninsu da jami'an tsaro, kuma za a yi ne a tsakanin nan da nan, suka yi maki ja a taswirar wuraren da suka lissafa. Sai kuma ranar aka lura da cewa duk wuraren da suka ambata din nan duk an je an jibge sojoji. Kaga sun shirya mashi kenan.

Jagora ya bayyana yadda sojoji suka bude wuta a Muzaharar, wadda sai da aka zabi inda aka lura cewa ba su jibge soja a wajen ba, amma suka bayyana suka yi ta'addanci akan 'yan uwa ta hanyar bude wuta ta gaba da bayan Muzaharar.

Daga ta'addancin sojojin Nijeriya a rannan, yace: "Kun ga wani hoto da aka nuna sojojin suna dukan wata yar uwa, su bakwai da sanduna, ita kadai, suna kokarin su fizge mata Hijabi, tana fisgewa tana rufe kanta, suna dukanta. Ka ga jarumai, masu gadin shugaban ƙasa! Babban kwamandan soja! Jarumawa! Sai su masu dukan soja! TIR! Wadannan tsinannu la'anannu! Lalacewa ya kai irin wannan? Mutum ya lalace irin wannan? Ya zama banza hofi irin wannan? Baka da wani karfi sai nuna karfi akan wanda bashi da ko makami yana tafiya? Har ace wai ku mazaje ne, amma ku far wa mace da duka? To Jarumtakar sojojin Nijeriya kenan".

Shaikh Zakzaky ya tambaya; "Me ya kawo masu gadin shugaban kasa kan titi suna harbi?" Yace, to wannan karon sai suka mana ya ma fi abin da suka yi mana a shekarar 2014 a Zaria, domin wancan da suka kashe mutane sun bar mana, mun je mun kwasa muka yi janazarmu, amma wannan karon sai suka kwashe duk wanda suka iya dauka, sai ya zama mun samu mutum 5 da farko, daga baya daya ya cika, aka samu mutum shida a hannunmu da muka musu jana'iza, amma zancen nan da muke ana cewa akwai mutum 20 da suka kashe suna hannunsu.

Shaikh Zakzaky ya yi tsokaci, tare da Allah wadai da kisan al'umma da aka yi a Kudu, inda ya bayyana duk kisa kisa ne, kuma abin Allah wadai ne. Yace: "Don ne mutum zai kau da kai daga wani kisan kai din? Mu ba yadda za a yi a yi kisan kai mu yi shiru, wannan abin da aka yi na kona mutane ya tada mana hankali, kuma mun yi magana a kai, amma mu abinda aka yi mana, kowa sai ya yi shiru”.

Shaikh Zakzaky (H) ya ci gaba da bayani yana mai cewa: “Idan har za ka yarda a kashe wani, wani ne baka yarda ba, to da sauranka, watarana kai ma za a kashe ka. Duk inda aka yi kisa sai a ce ba a yarda da kisan kai ba. Ballantana kuma ace jami'i tsaro ne wanda ya kamata ya tsare doka, amma shi ke kisan da kansa”. 

Ya jaddada cewa: “In mu ne, ba yadda za a yi a kashe wani, ko meye addininsa, ko meye kabilarsa, ba yadda za a yi mu goyi baya. Ba kuma yadda za a yi ace mun yi farin ciki da mutuwar wani, ballantana kashe wani".

A karshe, Jagora (H) ya tunawa jami'an tsaron da ire-iren ƙarshen da magabatansu daga jami'an tsaro suka rika yi a baya. Yace, kuma hankali bai nuna mutum zai kashe mutane ya koma ya rayu da iyalansu a gari ko unguwa guda ba nan gaba. Tare da jaddada ma azzalumai cewa, lallai zalunci baya dauwama, kuma ba makawa za a koma ga addinin Allah, addini zai kafu daram ya yi iko da wannan al'umma.

Allahumma Swalli Ala Muhammad Wa'ahli Muhammad Wa'ajjil Farajahum, Wansur Imamuna Zakzaky (H).

Allah Ya Ƙara Maku Lafiya Da Nisan Kwana Sharfudden Na Allah Bawan Allah.

@Szakzakyoffice

Shawwal/1446

Your Comment

You are replying to: .
captcha