Alal aqalla shahidai hudu ne aka samu a harin da Isra'ila ta kai a Khan Yunis kana wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wannan harin da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan tantunan 'yan gudun hijirar Falasdinu a yankin Qayzan Abu Rashwan da ke kudancin Khan Yunus, wasu daga cikinsu kuma kananan yara ne.
An tabbatar da cewa fiye da mutane 4 ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon harin bam da aka kai kan tantunan ‘yan gudun hijira a zirin Gaza, majiyoyin Falasdinawa sun bayar da rahoton cewa, wani hari da jiragen yakin sahyoniyawa suka kai a wani tanti na ‘yan gudun hijira a yammacin birnin Khan Yunus, inda ya kashe ‘yan uwa guda hudu tare da jikkata wasu da dama.
Your Comment