A yau ne sojojin Isra'ila suka shadantar da kananan yara Falasdinawan da ke sanye da sabbin tufafi don murnar sallar Idi.
Duk da hare-haren ta'addancin Isra'ila a ga al'ummar Palastinu Mutane 120,000 ne suka gudanar da Sallar Idi a Masallacin Al-Aqsa Dubun dubatar Falasdinawa ne suka gudanar da Sallar Idi a Masallacin Al-Aqsa a safiyar yau Lahadi, duk kuwa da hani da tsauraran matakan da sojojin mamaya suka dauka.
A cewar cibiyar yada labarai ta Falasdinu, hukumar da ke kula da kare hakkin Musulunci ta birnin Kudus ta sanar da cewa masallata 120,000 ne suka halarci wannan masallaci mai albarka.
Dakarun mamaya sun kafa shingen karfe a kewayen tsohon birnin Kudus da hanyoyin shiga, da kuma kan tituna da kofofin birnin Kudus, musamman ma a mashigar Babul-Amoud, Babul-Asbat, da Babul-Sahra.
Wadannan dakarun an jibge su a kewayen tsohon birnin Kudus da kuma masallacin Al-Aqsa, kuma sun sanya dokar hana zirga-zirgar masallata a kofar shiga masallacin.
Sai dai a harabar masallacin an ga dimbin jama'a daga birnin Kudus da kuma yankunan Palastinawa da aka mamaye da suka zo wannan wuri mai tsarki don gudanar da sallar asuba da na Idi, inda suka rika kwalla takbirai a kan titunan birnin da kuma cikin masallacin.
A cikin hudubar Sallar Idi, Malamin Masallacin Al-Aqsa ya yi ishara da muhimmancin watan Ramadan da kuma Idin karamar Sallah tare da jaddada wajibcin Musulmi su yi riko da ibadar wannan rana.
Yayin da yake ishara da yanayi na musamman na bukukuwa a Falasdinu da Kudus, Sheikh Yousef Abu Sunina ya ce: “Abin takaici, bukukuwan suna wakana ne a lokacin da muke kokarin jin dadi, amma idan muka dubi halin da musulmi suke ciki a wannan kasa mai tsarki, sai mu ga rushewa ta ko'ina, da yin kaura, da kuma bala’o’i.
Ya kara da cewa: "Makiya sun kwaɗaita akanmu, wasu kuma sun samu kwarin gwiwar kai mana hari, har ta 'ya'yanmu suna cikin bakin ciki da fargaba.
Your Comment