1 Afirilu 2025 - 16:59
Source: ABNA24
Harin Da Isra'ila Ta Kai A Yankin Beirut Yayi Sanadiyyar Shahadar Manyan Jami'an Hizbullah 3 + Bidiyo

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kai hari ta sama kan wani gini a yankin kudancin birnin Beirut. Inda mutane 4 su kai shahada 6 suka jikkata

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (ABNA) ya habarta cewa: gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta sake kai hari a yankunan kudancin birnin Beirut, inda ta keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta sau da yawa kamar yadda Kamfanin dillancin labaran shafin yada labarai na Al-Mayadeen ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari kan benaye da dama na wani gini da ke wani katafaren unguwar da ke yankunan kudancin birnin Beirut.

Bayan 'yan mintoci kaɗan, sojojin Isra'ila sun yi iƙirarin cewa, a ƙarƙashin jagorancin Shin Bet (Hukumar tsaron cikin gida ta Isra'ila), ta kai hari kan wata rundunar Hizbullah ta Lebanon a yankin.

A cewar majiyoyin Lebanon, bayan harin baya-bayan nan da Isra'ila ta kai a kudancin birnin Beirut, an kashe mutane hudu tare da jikkata wasu shida.

A baya dai sojojin Isra'ila sun sanar da kashe wani fitaccen shugabannin Hizbullah a yankin "Dahiya" da ke kudancin birnin Beirut.

A cikin wata sanarwar gaggawa da sojojin Isra'ila suka fitar sun sanar da cewa: Mun jefa bama-bamai kan wani shugaban kungiyar Hizbullah a yankunan kudancin kasar da a baya-bayan nan ke taimakawa Hamas da kuma barazana ga tsaron Isra'ila. Saboda wannan dalili ne haka nan take sojojin suka dauki matakin kawar da shi.

A cewar sabon sanarwar da ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta fitar, harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan wannan ginin da ke unguwar ya yi sanadin shahidai akalla 4 da jikkata wasu 6.

An tabbatar da Shahadar Hasan Badir da dansa a harin da Isra'ila ta kai a daren jiya a yankunan kudancin kasar Labanon wanda aka ce shi ne mataimakin shugaban ofishin Falasdinawa a kungiyar Hizbullah ya yi shahada tare da dansa Ali.

Hajj Ammar Al-Dabbas kwamandan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da Hajj Samih Al-Dalloul kwamandan kungiyar Hamas ta Falasdinu suna daga cikin wadanda su ka yi shahada a wannan hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai a yankin kudancin birnin Beirut a daren yau.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto majiyar kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa an kashe Hasan Badir mataimakin kungiyar Hizbullah mai kula da al'amuran Palasdinawa a wani harin bam da aka kai a yankunan kudancin birnin Beirut a ranar Talata.

Martanin Da Hukumomi Suka Mayar Dangane Da Wannan Mummunan Hari:

Shugaban Kasar Labanon:

A halin da ake ciki kuma shugaban kasar Labanon Joseph Aoun a cikin wata sanarwa da ya fitar game da harin ya ce: Harin na Isra'ila babban gargadi ne game da boyayyar aniya kan Lebanon.

Shugaban na Lebanon ya yi Allah wadai da harin na yau, ya kuma yi kira da a gujewa duk wani cin zarafi na keta iyaka na hukumar kasar daga ketare ko kuma daga cikin gida.

Shugaban kasar Labanon: Hare-haren Isra'ila wata alama ce ta gargadi game da mugun nufi da gwamnatin kasar ke da shi kan kasar Labanon Da yake yin Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a baya-bayan nan, shugaban kasar Labanon Joseph Aoun ya bayyana wadannan ayyuka a matsayin wani babban gargadi game da mugunyar manufar gwamnatin kasar a kan Labanon.

Ya ci gaba da cewa: "Ci gaba da cin zarafi da Isra'ila ke yi na bukatar mu kara kaimi wajen samun goyon bayan kasashen duniya kan 'yancin Lebanon na samun cikakken 'yancin cin gashin kanta. "Tare da hadin gwiwar gwamnati da firaministan kasar, za mu dakile duk wani yunkuri na lalata wannan babbar dama ta ceto Lebanon".

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka:

Ita kuwa Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta goyi bayan harin da Isra'ila ta kai kan kasar Labanon Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fito karara ta bayyana goyon bayanta ga harin da sojojin mamaya na Isra'ila suka kai a birnin Beirut a yau.

Hakan dai na faruwa ne duk da cewa jami'an kasar Labanon din sun bayyana harin da cewa ya sabawa kudurin kwamitin sulhu mai lamba 1701. Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, yayin da ta bayyana goyon bayan kasarta ga hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi, ta dauki matakin a matsayin martani ga harin makami mai linzami.

Ya kamata a lura cewa kungiyar Hizbullah ta musanta cewa tana da alaka da harin makami mai linzami na baya-bayan nan da aka kai kan yankunan da aka mamaye.

Wakilan Hizbullah:

Wakilin Hizbullah: Hakurinmu na da Iyaka. Wakilin Majalisar Hizbullah na Labanon Ali Ammar ya yi gargadi, bayan harin makami mai linzami da Isra'ila ta kai a yankunan kudancin birnin Beirut, cewa "Hakurin gwagwarmaya yana gab da karewa.

Shima Ibrahim al-Moussawi, wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Lebanon: Hare-haren da Isra'ila ta kai a yankunan kudancin kasar wani babban wuce gona da iri ne harin da aka kai kan fararen hula a yankunan kudancin kasar abin zargi ne kuma ya kara dagula lamarin zuwa wani mataki mai hadari.

Dole ne gwamnati ta dauki matakin dora alhakin laifin cin zarafin da ake yi wa yankunan kudancin kasar.

Ba za mu iya yin shiru ba game da ci gaba da kashe fararen hula da Isra'ila ke yi a kudancin Lebanon.

Makiyan gaban ta hanyar ci gaba da kai hare-harensa da cin zarafi a kudanci, Bekaa, da yankunan kudancin, ya sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta.

Mun jajirce akan alkarinmu, kuma gwamnatinmu tana da cikakkiyar dama bayan wannan cin zarafi. Amma mu ba masu son yaqi bane.

Wannan abin ba abune da zai zaa lamunce shi ba ace al’umma tana gani ana kai wa ‘ya’yanmu hari a lokacin da suke barci, kuma babu hujjar da za’a fake da ita akan kai wa fararen hula hari.

Your Comment

You are replying to: .
captcha