30 Maris 2025 - 10:42
Source: ABNA24
Yemen Ta Kai Harin Makamai Masu Linzami Da Jiragen Yaƙi Kan Jirgin Yaƙin Amurka 

Kasar Yemen ta kai wani gagarumin hari kan jirgin ruwan yakin Amurka da makami mai linzami da jirage marasa matuka

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Kakakin rundunar sojin Yemen Yahya Saree ya bayyana cewa, sojojin Yaman sun kai hari da makami mai linzami da kuma jiragen kunar bakin wake kan wani jirgin ruwan yakin Amurka.

Da yake fitar da sanarwa a safiyar yau Lahadi, Kakakin Rundunar Yaman Yahya Saree ya bayyana cewa, sau 3 ne sojojin kasar Yemen din suka yi arangama da jirgin ruwan mai ɗaukar jiragen Amurka USS Harry S da wadansu jiragen da ke masa rakiya a takun Bahri maliya cikin a wanni 24 da suka gabata.

Saree ya jaddada cewa, "Tare da taimakon Allah Madaukakin Sarki, sojojinmu suna cikin amana da kuma yanayin da ya kamata wajen tunkarar hare-haren da Amurka ke kaiwa kasarmu Yemen a mako na uku a jere".

Ya kara jaddada cewa za su ci gaba da fadada ayyukan tsaro da kuma "rama tashin hankali da tashin hankali".

"Ba za mu taba ja da baya daga goyon baya da bayar da taimako ga al'ummar Palastinu da ake zalunta ba har sai an daina kai hare-hare tare da kawar da kai hare-hare a zirin Gaza.

Al'ummar kasar Yemen sun bayyana goyon bayansu a fili ga gwagwarmayar Falasdinu wajen fuskantar yan mamayar Isra'ila tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da mummunan yaki a kan Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba bayan da 'yan gwagwarmayar Falasdinawa na yankin suka kai wani harin ba-zata mai suna Guguwar Aqsa, kan mamaya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha