Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (ABNA) ya habarta cewa ofishin yada labaran Palasdinu ya fitar da alkaluman kididdiga na baya-bayan nan game da yaki da kisan kiyashin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a zirin Gaza, wanda aka fara kwani 534 da suka gabata kuma ya ke ci gaba har zuwa yanzu.
Rubutun wannan rahoto, wanda ke gabatar da kididdiga masu tayar da hankali game da halin jin kai da zamantakewa a Gaza, shi ne kamar haka:
– Daga ranar Asabar, 7 ga Oktoba, 2023 zuwa yau Lahadi, 23 ga Maris, 2025 (na tsawon kwanaki 534)
- kwanaki 534 na kisan kiyashi da share tsatso.
- Sojojin mamaya na Isra'ila sun kashe mutane 12,000.
– An tabbatar da yin shahadar shahidai 61,221.
- Fiye da 11,200 sun bace, ciki har da shahidan da ba’a iya kai su asibiti ba da kuma wasu da ba a san makomarsu ba.
- Shahidai 50,021 wadanda aka yiwa rajistar gawarwakinsu a asibitoci (Ma'aikatar Lafiya).
- Kisan 11,850 akan iyalai gaba daya Falasdinawa (Ma'aikatar Lafiya).
- An share iyalan Falasdinawa 2,165 gaba daya daga samuwa, wanda ya hada da kashe uba, uwa da daukacin 'yan uwa, jimillar shahidai 6,161 (Ma'aikatar Lafiya).
Iyalan Falasdinawa 5,064 da mamayar ta share su, ya rage saura mutum daya kacal, wanda adadin shahidai a wadannan iyalai ya zarce 9,272 (Ma'aikatar Lafiya).
- Yara shahidai 17,954.
- Jarirai 274 da suka yi shahada a lokacin haihuwa.
– Jarirai 876 ‘yan kasa da shekara daya da suka yi shahada a wannan kisan kare dangi.
- Shahidai 52 saboda rashin abinci mai gina jiki da kuncin yunwa.
- Shahidai 17 saboda sanyi a cikin tantunan 'yan gudun hijira, ciki har da yara 14.
– Mata 12,365 ne suka yi shahada a hannun ‘yan mamaya na Isra’ila.
- Ma'aikatan lafiya 1,394 suka yi shahada (Ma'aikatar Lafiya).
– Jami’an kashe gobara ne suka yi shahada.
– ‘Yan jarida 206 ne suka yi shahada a hannun ‘yan mamaya.
– Shahidai 743 daga jami’an tsaro da masu aikin agaji.
- An kai hare-hare 154 kan jami'an tsaro da ke kare ayarin motocin agaji.
- Kaburbura 7 na gungun jama'a da sojojin isra’ila suka tona a cikin asibitoci.
- An gano gawarwakin shahidai 527 daga kaburbura 7 da ke cikin asibitoci.
- 113,274 da suka jikkata da kuma wadanda suka samu raunuka a asibitoci (Ma'aikatar Lafiya).
- 17,000 sun ji rauni suna buƙatar dogon lokaci wajen yi masu magani (Ma'aikatar Lafiya).
- 4,700 masu raunin da aka yankewa wata gaba ta jikinsu, 18% daga cikinsu yara ne (Ma'aikatar Lafiya).
- Fiye da kashi 60% na wadanda abin ya shafa mata ne da yara.
– ‘Yan jarida 400 da jami’an yada labarai suka jikkata.
- Cibiyoyin 'yan gudun hijira 226 da Isra’ila ta kai wa hari.
- Kashi 10 cikin 100 na kasar Gaza 'yan mamaya sun ayyana shi a matsayin "yankin jin kai" wanda hakan ba daidai ba ne.
- Yara 39,384 ne ke rayuwa a yanzu ba tare da iyaye ko daya ba.
– Mata 14,323 suka rasa mazajensu a wannan kisan kiyashin.
- Yara 3,500 ke cikin hadarin mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki da yunwa.
- marasa lafiya 22,000 suna buƙatar magani a ƙasashen waje.
- marasa lafiya 13,000 da suka ji rauni wadanda suka kammala dukkan shirye shirye da suke jiran tafiya.
- 12,500 masu fama da cutar daji wadanda ke cikin hadarin mutuwa saboda rashin magani.
- Marasa lafiya 3,000 da ke fama da yanayi daban-daban waɗanda ke buƙatar magani a ƙasashen waje.
- 2,136,026 na cututtuka masu yaduwa gudun hijira (Ma'aikatar Lafiya).
- 71,338 lokuta na kamuwa da cutar hanta saboda yawan yin hijira.
- Kimanin mata masu juna biyu 60,000 ne ke cikin hatsari saboda rashin kula da lafiya.
- 350,000 marasa lafiya na yau da kullun suna cikin haɗari saboda masu hana shigo da magunguna.
- Fursunoni 6,628 da mamaya suka kama daga Gaza.
- An kama ma'aikatan lafiya 360, ciki har da likitoci 3 da aka kashe a gidan yari.
– An kama ‘yan jarida 48, wadanda aka san sunayensu.
– An kama jami’an kashe gobara 26.
- Kimanin mutane miliyan 2 ne suka rasa matsugunansu a Gaza.
- Tantuna 110,000 da suka lalace kuma ba su dace da rayuwa acikinsu ba ga mutanen da suka rasa muhallansu ba.
- Iyalai 280,000 a Gaza suna buƙatar tantuna, ko gidajen tafi da gidanka.
- Gine-ginen gwamnati 221 da mamaya suka lalata.
– Makarantu da jami’o’i 139 da ‘yan mamaya suka lalata su gaba daya.
– Makarantu da jami’o’i 359 da ‘yan mamaya suka lalata wani bangarensu.
– Dalibai 12,900 ne suka yi shahada a hannun ‘yan mamaya.
- Dalibai 785,000 ne aka hana su karatu saboda mamaya.
- Malamai da ma'aikatan ilimi 800 ne suka yi shahada.
- Masana kimiyya, malamai, malaman jami'a 150 wadanda 'yan mamaya suka kashe.
- Masallatai 825 da aka lalace gaba daya.
- Masallatai 161 da suka lalace sosai kuma suna bukatar sake gina su.
- Coci 3 da aka kaiwa hari aka lalata su.
- Makabartu 19 da aka lalata wani bangare ko gaba daya daga cikin makabartu 60.
- Gawarwaki 2,300 da mamaya suka sace daga makabartun Gaza.
- Kimanin gidaje 165,000 ne suka lalace gaba daya.
- Kimanin gidaje 115,000 sun lalace sosai kuma ba za su iya zaunuwa ba.
- Kimanin gidaje 200,000 ne aka lalata wani bangare.
- Sama da ton 100,000 na bama-bamai ne aka jefa a Gaza.
- asibitoci 34 da aka kona, an kai musu hari, ko kuma su ka dena aiki.
- Cibiyoyin lafiya 80 da mamaya suka rufe.
- Cibiyoyin lafiya 162 aka kaiwa hari.
- Motocin daukar marasa lafiya 138 aka kaiwa hari.
- 206 wuraren tarihi da al'adu da aka lalata.
– An lalata hanyoyin samar da wutar lantarki mai tsawon kilomita 3,700.
– An lalata taransifoma masu rarraba wutar lantarki guda 2,105.
- An lalata hanyoyin sadarwa na ruwa mita 330,000.
- An lalata hanyoyin sadarwa na tace ruwa mita 655,000.
- An lalata tituna da tituna mita 2,846,000.
– An lalata wuraren wasanni da filayen wasanni 42.
– An lalata rijiyoyin ruwa 719 tare da fitar da su daga aiki.
- Sama da kashi 88% na ababen more rayuwa na Gaza sun lalace.
- Fiye da dala biliyan 41 a asarar farko kai tsaye daga kisan kiyashin.
Wadannan kididdigar na nuni da irin mawuyacin halin da ake ciki da kuma na jin kai a Gaza tare da kwatanta bukatar kulawar gaggawa da daukar matakai daga kasashen duniya.
Ranar bugawa: Yau Lahadi, Maris 23, 2025, daidai da Farvardin 3, 1404
Your Comment