12 Maris 2025 - 01:50
Source: ABNA24
Yadda Al’ummar Kasar Yaman Suka Fito Domin Nuna Goyon Bayansu Ga Matakin Sojojin Kasar

Al'ummar kasar Yemen sun nuna goyon bayansu ga matakin da sojojin kasar suka dauka kan gwamnatin sahyoniyawa na ci gaba da kai hare-hare ga jiragin ruwan Isra’ila

Al'ummar kasar Yemen sun gudanar da wani gagarumin gangami a babban birnin kasar, Sanaa, domin nuna goyon bayansu ga matakin da kungiyar Ansar Allah ta dauka na sake ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

 Al'ummar kasar sun fito suna masu jaddada cewa za su ci gaba da goyon bayan al'ummar Palastinu da ake zalunta.

Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar a safiyar yau Laraba cewa, kasar ta sake sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa masu alaka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin tekun Bahar Rum, Tekun Arabiya, da mashigin Babul-Mandab.

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya yi gargadin a yammacin ranar Juma'a cewa idan har gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ba ta kawo karshen kawanya da kuma barin gudanar ayyukan jin kai da ake kai wa Gaza cikin kwanaki hudu masu zuwa ba, to kungiyar za ta koma aikin sojan ruwa a kan Isra'ila.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha