Harkar Mujahiddin Falasdinu ta yi maraba da matakin da kasar Yamen ta dauka kan jiragen ruwan yahudawan sahyoniya.
Harkar Mujahiddin Falasdinu ta yi marhabin da matakin da sojojin Yamen suka dauka na dawo da shingen jiragen ruwa da kuma haramta zirga-zirgar jiragen ruwa na Isra'ila a cikin ruwan yankin, tare da daukar wannan mataki a matsayin wani mataki na tinkarar munanan manufofin yahudawan sahyoniyawan a Gaza.
Kungiyar ta fitar da wata sanarwa inda ta jaddada cewa matakin jarumta na kasar Yamen wani kalubale ne ga gwamnatin sahyoniyawa da kuma karya shiru da kasashen duniya suke yi kan laifukan da take aikatawa, sannan ta sanar da cewa wannan matsaya alama ce ta ci gaba da goyon bayan kasar Yamen ga al'ummar Palastinu da kuma gwagwarmaya kan makiya yahudawan sahyoniya.
Har ila yau Harkar Mujahid ta yi kira ga al'ummar musulmi masu rai da rayuwa da su taka rawar gaske wajen tallafawa al'ummar Palastinu tare da yin kira ga al'ummar duniya masu 'yanci da su matsa lamba kan gwamnatin yahudawan sahyoniya da magoya bayanta da su share fagen dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar Palastinu.
Kungiyar Jihadil Islam Ita Ma Ta Goyi Bayan Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Yaman Akan Jiragen Ruwan Isra'ila
Kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu ta fitar da wata sanarwa inda ta yi maraba da sanarwar da sojojin Yamen suka yi na sake kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra'ila a tekun Bahrul Ahmar da Arab da kuma sanya sabon shingen da sojojin gwamnatin kasar suka yi bayan kin barin isar kayayykin agajin jin kai shiga Gaza da kuma sabon kawanyar da Isra’ila tai wa Falasdinawa da suke wannan yankin.
Kungiyar ta dauki matakin da sojojin kasar Yemen suka dauka a matsayin wani mataki na jajircewa wajen matsin lamba ga gwamnatin sahyoniyawan da magoya bayanta da su bude mashigar da kuma ba da damar shigar da kayayyakin jin kai a zirin Gaza da suka yi wa kawanya.
Harka Islamiyya a cikin bayaninta ta jaddada cewa, wannan matsayar da ta dauka na nuni da asali da jajircewar al'ummar kasar Yemen wajen goyon bayan al'ummar Gaza da goyon bayan al'ummar Palastinu da gwagwarmaya.
Har ila yau Harkar ta sanar da cewa, wannan mataki yana jaddada hadin kai wajen fuskantar yan mamaya da zalunci tare da sake tabbatar da tsayin dakan al'ummar kasar Yemen na goyon bayan Palastinu da kuma tinkarar wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawa.
Kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu, yayin da take yaba wannan tallafin goyon bayan da ake samu mai yawa, ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da su dauki irin wannan matsayi.
Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar a safiyar yau Laraba cewa, kasar ta sake sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa masu alaka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin tekun Bahar Rum, Tekun Arabiya, da mashigin Babul-Mandab.
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya yi gargadin a yammacin ranar Juma'a cewa idan har gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ba ta kawo karshen kawanya da kuma barin gudanar ayyukan jin kai da ake kai wa Gaza cikin kwanaki hudu masu zuwa ba, to kungiyar za ta koma aikin sojan ruwa a kan Isra'ila.
Your Comment