12 Maris 2025 - 11:13
Source: ABNA24
Birnin Rafah Yana Cikin Mawuyacin Halin Tabarbarewa/Kashi 70 Na Mazaunasa Har Yanzu Suna Gudun Hijira

Mashigar ta Rafah ita ce mashigar zirin Gaza daya tilo zuwa kasashen waje, kuma tana da matakukar muhimmanci ga Falasdinawa saboda sabanin sauran mashigogin, ita ba ta karkashin ikon Isra'ila kai tsaye.

Gwamnan birnin Rafah ya jaddada cewa: Kashi 60 cikin 100 na birnin na karkashin ikon 'yan mamaya na Isra'ila ne: 'Yan mamaya har yanzu suna da iko da wutar lantarki a mafi yawan birnin kuma sun kasance gaba daya a yankin Salahad-Din.

Dr. Ahmed Al-Sufi, ya ce yarjejeniyar ta jaddada janyewar ‘yan mamaya bayan kwanaki 50, ya ce: “Wa’adin janyewar ya kasance ranar Litinin, amma ‘yan mamaya sun ki aiwatar da yarjejeniyar.

Al-Sufi ya kara da cewa: "Kashi 70 na mazauna Rafah har yanzu suna gudun hijira a yankin Mawasi da ke Khan Yunus kuma suna fuskantar mawuyacin hali na jin kai".

Da yake gargadin afkuwar rashin samun kayan jin kai, ya bayyana cewa ci gaba da mamayar 'yan mamaya zai kara ta'azzara rikicin da kuma kawo cikas ga kokarin maido da kwanciyar hankali.

Shin mashigar Rafah za ta dawo yadda ta ke kafin ranar 7 ga Oktoba?

Mashigar ta Rafah ita ce mashigar zirin Gaza daya tilo zuwa kasashen waje, kuma tana da matakukar muhimmanci ga Falasdinawa saboda sabanin sauran mashigogin, ita ba ta karkashin ikon Isra'ila kai tsaye.

 Sai dai kuma sake bude ta na baya-bayan nan ba ya nufin an kawo karshen rikicin da ake yi a mashigar ba ne, domin har yanzu ana fama da rikicin siyasa tsakanin Falasdinu, Masar da Isra'ila.

A shekara ta 2005, Isra'ila ta janye daga zirin Gaza, kuma an rattaba hannu kan yarjejeniyar gudanar da mashigar ta Rafah, wadda a karkashinta masu sa ido na kasa da kasa za su sanya ido kan zirga-zirgar ababen hawa da kuma gudanar da harkokin Falasdinawa ba tare da jami'an tsaron Isra'ila ba.

A shekara ta 2007, bayan da Hamas ta hau kan karagar mulki a Gaza, an dakatar da aikin kungiyar EU a mashigar, sannan aka sauya tsarin gudanarwarta.

Daga shekarar 2007 zuwa 2023, Masar ta sha rufe mashigar ta kuma sanya takunkumi, yayin da ita ma Isra'ila ta rika sanya ido a fakaice wajen shiga da fitan mutane.

Bayan 7 ga Oktoba, 2023, biyo bayan Guguwar Aqsa (Dufanul Aqsa), Isra'ila da Masar sun tsaurara matakan tsaro kuma an rufe mashigar Rafah gaba daya, sai dai wadanda suka biya kudade masu yawa don fita.

A cikin Mayu 2024, Isra'ila ta mamaye tare da jefa bama-bamai a mashigar Rafah, ta hana wucewar marasa lafiya da batutuwan na gaggawa.

A shekarar 2025, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wuta, an sake bude mashigar, amma tare da sabbin sharuddan da ke ci gaba da kasancewa karkashin ikon Isra'ila.

Kalubalen Kula Da Mashigar Rafah Bayan An Bude Shi

Duk da sake buɗe mashigar wucewar, akwai sauran ƙalubale da yawa:

Isra'ila tana da iko kan shige da fice jerin fasinjoji: Duk wani da zai fita daga Gaza yana buƙatar amincewa daga hukumar tsaron Isra'ila (Shabak), wanda ke nuni da ikon Tel Aviv akan wannan mashigar, koda ba tare da kasancewar dakarunta kai tsaye ba.

Matsayin Masar:

Alkahira, wacce a baya ta ba wa wasu damar fita bayan ta karbar kudade masu yawa, a yanzu haka ma tana tabbatar da jerin fasinjojin tare da hadin gwiwar Isra'ila.

Kasancewar Tarayyar Turai:

Kungiyar Tarayyar Turai bayan ta dauki shekaru 18 tana a matsayin mkai sa ido, amma rawar da take takawa ba ta da yawa.

Matsayin Hukumar Falasdinu:

 Wannan cibiya da Isra'ila ta gabatar a matsayin madadin kungiyar Hamas wajen kula da mashigar, tana da takaitaccen tasiri a Gaza.

Makomar mashigar Rafah da abubuwan da suka faru

Ci gaba da halin da ake ciki:

Gudanarwar Isra'ila kai tsaye tare da kulawar EU tare da hadin gudanarwar PA.

Yiwuwar rikici tsakanin Hamas da PA:

 Idan PA na son samun ƙarin iko a Gaza, zata a iya ƙara samun tashin hankali da Hamas.

Matsayin Masar a nan gaba:

 Alkahira na iya amfani da wannan sashe wajen yin matsin lamba na siyasa a kan kungiyoyin Falasdinu.

Haɓakar taka rawar kasa da kasa na kasashen duniya:

Mai yiyuwa ne Majalisar Dinkin Duniya ko wasu kasashe za su taka rawar gani wajen sanya ido a kan mashigar a nan gaba.

Mashigar Rafah ta kasance wani muhimmin batu a daidaiton siyasar Gaza. Yayin da sake bude ta wani mataki ne mai kyau ga al'ummar Gaza, ikon Isra'ila, tasirin Masar, da gudanar da harkokin PA na ci gaba da haifar da manyan kalubale.

 Makomar wannan mashigar ta dogara ne da nasarar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da tattaunawar siyasa, da ci gaba a fagen fafatawa a Gaza.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha