10 Maris 2025 - 09:40
Source: ABNA24
Bidiyon Yadda Isra’ila Ta Mayar Da Sansanin Nour Shams

Motocin Buldozar yakin haramtacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da sauya fasali da yanayin sansanin a karkashin manufarsu na matakan tsaro da shimfida hanyoyi a tsakiyar sansanin tare da rushe gidajen Falasdinawa da wuraren hidima. An ruguje gidaje gaba daya wasu kuma sun lalace.

Isra’ila Yar Mamaya ta ruguza gidaje tare da barna mai yawa a sansanin Nour Shams da ke Tulkarm,a arewacin gabar yammacin kogin Jordan. Wasu daga mazauna Falsdinuwa bayan da aka ba su izinin isa gidajensu, sun kadu matuka da irin barnar da aka yi a gidajensu da wurare da sauran gidajen da ba a lalata ba.

Wasu kuma sun yi kokarin kwashe wasu kayansu daga sansanin. Akwai wadanda ba su sami wani abu ba, dukkan kjayan gidan da suka hada da Injin wanke-wanke, firij, da allunan duk sun lalace kuma.

Motocin Buldozar yakin haramtacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da sauya fasali da yanayin sansanin a karkashin manufarsu na matakan tsaro da shimfida hanyoyi a tsakiyar sansanin tare da rushe gidajen Falasdinawa da wuraren hidima. An ruguje gidaje gaba daya wasu kuma sun lalace.

Wata mata BaFalasdiniya tana cewa: Alhamdu lillahi, amma muna bukatar hakuri, da irada da halin kirki. Abu mai mahimmanci shi ne mu ci gaba da juriya matuƙar ɗabi'armu ta juriya tana da girma. Ba mu damu da wani abu ba. Mazauna sansanin. Sun dauki abin da ke faruwa da su a matsayin yunkurin share da kasarsu daga samuwa.