6 Maris 2025 - 06:06
Source: ABNA24
Hamas: Barazanar Trump Ba Ta Da Wani Amfani / Babu Fursunonin Da Za A Saki Ba Tare Da Yarjejeniya Ba 

Hamas ta tabbatar da cewa: Ana ci gaba da kokari na masu shiga tsakani na aiwatar da dukkan matakai na yarjejeniyar

Dr. Sami Abu Zuhri, ɗaya daga cikin shugaban kungiyar Hamas, ya jaddada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Shahab cewa barazanar da Donald Trump ke yi wa Hamas ba ta wani muhimmanci, kuma ba ta da amfani, kuma idan har barazanar ta zama dole, to ya kamata a yi wa wadanda suka ki aiwatar da yarjejeniyar, ba wadanda suka yi riko da ita ba.

Hamas dai ta jajirce kan yarjeniyoyi kuma ta kuduri aniyar ci gaba da bin wannan tafarki, amma harshen barazana ba wai kawai ba ya tsorata mu ba ne, a'a sai dai ma yana kara dagula lamarin ne.

Ya kamata kowa ya sani cewa babu wani fursuna da za a saki ba tare da aiwatar da yarjejeniyar ba.

Hamas ta tabbatar da cewa: Ana ci gaba da kokari na masu shiga tsakani na aiwatar da dukkan matakai na yarjejeniyar

Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya jaddada cewa masu shiga tsakani za su ci gaba da tuntubar juna domin tabbatar da aiwatar da sauran matakan da suka rage na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma tilastawa gwamnatin Isra'ila fara tattaunawa a mataki na biyu na yarjejeniyar.

Ya kara da cewa: Hamas ta jaddada kudurinta na cimma matakai daban-daban na yarjejeniyar, muna fatan tuntubar masu shiga tsakani za su kai ga kammala aiwatar da matakan da gwamnatin sahyoniya ta dauka.

Tattaunawa tsakanin shugabannin Hamas da wakilan Masar, Qatar da Amurka

Majiyoyin Masar sun sanar da wani sabon zagayen tattaunawa tsakanin shugabannin Hamas da wakilan Masar, Qatar, da Amurka.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto cewa: wasu jami'an kasar Masar guda biyu sun rubuta cewa batun tattaunawar da ya hada da Stephen Whitakoff wakilin shugaban Amurka na musamman kan yankin gabas ta tsakiya shi ne mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza.

Wadannan majiyoyin da ba a bayyana sunayensu ba, yayin da suke yin nazari mai kyau kan wadannan tattaunawa, sun bayyana cewa, an tattauna irin salon gwamnati a Gaza da sunayen mutanen da za su gudanar shugabancinta.

Your Comment

You are replying to: .
captcha