6 Maris 2025 - 14:00
Wani Fursunan Falsɗinawa Yayi Shahada A Gidan Yarin Isra'ila 

An fitar da sanarwa shahadar wani fursuna Bafalasdine a gidan yarin Isra'ila

Hukumar kula da harkokin farar hula ta Falasdinu, tare da hukumar kula da fursunoni da kungiyar fursunoni ta Falasdinu, sun sanar da cewa Ali Ashour Ali Al-Batsh, fursuna mai shekaru 62 daga Gaza, ya yi shahada a ranar 21 ga Fabrairu, 2025, a asibitin Soroka.

A kwanakin baya ne aka kai shi asibiti daga gidan yarin Negev, amma ya yi shahada sakamakon ta'addanci da azabtarwa da gwamnatin sahyoniya ta yi wa fursunonin.

An kama Ali al-Batsh ne a ranar 25 ga Disamba, 2023. Ya yi aure ya haifi ‘ya’ya shida.

Shi ne fursuna na hudu da ya yi shahada cikin kankanin lokaci, kuma bisa wannan kididdiga, adadin fursunonin Palastinawa da suka yi shahada tun farkon yakin kisan kare dangi ya kai 62, 40 daga cikinsu sun fito ne daga Gaza.

Wannan shi ne adadi mafi girma na tarihi na shahadar fursunoni a gidan yarin gwamnatin mamaya kuma yana a matsayin lokaci mafi muni a tarihin yunkurin fursunonin tun shekara ta 1967.

Hamas ta ce: ci gaba da aiwatar da hukuncin kisa kan fursunoni na nuni da irin ta'asar da gwamnatin sahyoniya ta ke aiwatarwa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta zargi gwamnatin mamaya da aiwatar da manufar "kisan mummuke cikin ruwan sanyi" kan fursunonin Palastinawa a gidajen yari, tare da jaddada cewa wadannan ayyuka na nuni da irin zaluncin 'yan mamaya da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma hakkokin fursunonin.

Ci gaba da aiwatar da siyasar aiwatar da hukuncin kisa sannu-sannu a hankali da gwamnatin yahudawan sahyoniya suke aiwatarwa a kan fursunoninmu da ke gidajen yari na nuni da irin zaluncin da wannan gwamnatin take da shi, da rashin mutunta dukkanin kimar bil'adama, da kin amincewa da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyoyin da suka shafi hakkokin fursunonin yaki.

Shahadar Ali al-Batsh, fursunan Palastinawa daga Jabalia da ke arewacin Zirin Gaza, a cikin gidajen yarin gwamnatin mamaya, ya samo asali ne daga manufofin siyasar gwamnatin masu tsattsauran ra'ayi na wannan gwamnati, wadda ta yi wa fursunonin Falasdinu hari ta hanyar cin zarafi da laifuka da suka hada da rashin kula da lafiya da gangan, gallazawa jiki da tunani, da hana su mafi ƙarancin hakkin dan Adam, da kuma tauye hakkin bil'adama.

Muna gargadi game da ci gaba da manufofin makiya na yunkurin kawar da fursunoni, kuma muna jaddada cewa wadannan ayyukan ba za su raunana nufinsu da fatan samun 'yanci na nan kusa ba.

Hamas ta yi kira ga al'ummar Palasdinu a duk yankunan da suke da su, da kuma cibiyoyin shari'a da na jin kai, da su kara kaimi wajen tallafa wa fursunonin da kuma kara matsa kaimi wajen kare manufarsu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha