Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wasu 'yan ta'adda da suka hada da maharan 14 suka shiga yankin sojoji a birnin Bannu da ke lardin Khyber Pakhtunkhwa a arewa maso yammacin kasar Pakistan, inda suka yi harbe-harbe tare da kai farmaki da wasu motoci biyu dauke da bama-bamai.
Harin dai ya faru ne daf da lokacin buda baki, inda wasu ‘yan kunar bakin wake biyu suka tayar da bama-bamai a gaban wani gidan farar hula.
Kafar yada labarai ta Pakistan Khorasan Daily ta rawaito cewa akalla fararen hula tara ne suka mutu sakamakon fashe-fashen, sannan shida daga cikin maharan sun mutu a arangama da jami'an tsaro.
Majiyar Pakistan ta sanar da cewa, wata kungiya mai suna Jaish-e-Fursan reshen Hafiz Gul Bahar na kungiyar ta'adda ta Tehreek-e-Taliban Pakistan, ta dauki alhakin hare-haren kunar bakin wake da aka kai yau a birnin Bannu.
Tashar yada labarai ta Geo Pakistan ta kuma yi ikirarin cewa akalla mutane 15 da suka hada da mata da yara da dama ne suka mutu yayin da wasu 25 suka jikkata a wadannan hare-haren.
Your Comment