Kamfanin dillancin labaran Shahab ya wallafa wadannan hotunan gwagwarmayar Palasdinawa da ke shirya wajen mika gawarwakin wasu 'yan Isra'ila hudu a yankin Bani Suhaila da ke gabashin Khan Yunis a kudancin zirin Gaza.
Tawagar Falasdinawa ta sanya wata tuta a wurin miƙa wasu fursunonin Isra'ila hudu a Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza, inda take ɗauke da cewa: Dawowar yaki na nufin komawar fursunonin Isra'ila a cikin akwatunan mutuwa.





