Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta maku cewa: Dakarun Izziddin Qassam sun sanar da cewa, mayakan wannan kungiya ta gwagwarmaya sun yi artabu da sojojin Isra'ila a kauyukan "Araba" da "Fahma" da ke yammacin birnin Jenin, inda suka kai musu farmaki da harsasai da bama-bamai na gida.
Zuwa yanzu ana ci gaba da gwabza fada tsakanin gwagwarmaya da sojojin yahudawan sahyoniya a yammacin Jenin
Jaridar Palestine Post ta yaɗa wasu bidiyoyi da ke nuna dakarun gwagwarmaya da a ka yi wa kawanya a wani gida a garin Barqin da ke yammacin Jenin a yankin yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye, har yanzu suna ci gaba da artabu da dakarun mamaya.
Yana da kyau a san cewa sojojin yahudawan sahyoniya sun kai hari kan wannan gida da harin makami mai linzami fiye da sau tara.
Hakanan kuma a wannan rahoton zaki ga bidiyoyin yadda motocin buldoza da kayan aikin sojan Isra'ila suke tafiya zuwa zuwa yammacin Jenin
Motocin buldoza da karin kayan aikin soji an tura su ne don karfafa sojojin yahudawan sahyoniya a yankin Barqin da ke yammacin Jenin a yammacin gabar kogin Jordan da suke kokarin mamayewa.
