17 Disamba 2024 - 18:26
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Karo Na Hudu Na Masu Fafutukar Raya Al'adun Arbaeen

An gudanar da taron kasa da kasa na masu fafutukar raya al'adu na kasa da kasa karo na 4 a birnin Mashhad daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Disamba tare da halartar mutane 300 na masu fafutukar al'adu, da masu Tabligi, da masu bincike, da kafofin watsa labarai da masu fafutukar a dandalin sada zumunta daga kasashen musulunci 10.

An gudanar da taron kasa da kasa na masu fafutukar raya al'adu na kasa da kasa karo na 4 a birnin Mashhad daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Disamba tare da halartar mutane 300 na masu fafutukar al'adu, da masu Tabligi, da masu bincike, da kafofin watsa labarai da masu fafutukar a dandalin sada zumunta daga kasashen musulunci 10.

Taro na musamman tare da yin shela mai ƙarfi mara misaltuwa

Muhammad Baqer Qalibaf shugaban majalisar addinin musulunci a sakon da ya aikewa wannan taro ya bayyana cewa: Taron miliyoyin masu tattakin Arba'in tare da halartar maziyarta na masu kaunar iyalan gidan tsarkaka da tsafta (a.s) babban taro ne da babu kamarsa. Da sunan taro mai girma da baya misaltuwa a cikin duniyar yada labarai, wadda shin ce fuskacin zukatan 'yantattun mutane na duniya a  wannan rayuwa.

Shi ma Hujjatul Islam wal-Muslimin Hamid Ahmadi shugaban kwamitin al'adu na shelkwatar Arbaeen ya bayyana a cikin wannan taron cewa: "Babban yunkuri na Arbaeen din Husaini wata babbar dama ce ta gabatar da al'adun Ashura a matsayin tushen wayewar zamani da gina al’ummar Musulunci”. Arbaeen ya kawo babban hadin kai a dukkan fagage tsakanin al'umma da gwamnatin Iran da Iraki, wanda wannan abin godiya ne.

Ya ci gaba da cewa: Daya daga cikin batutuwan da mahalarta taron masu fafutukar raya al'adu na Arbaeen suka yi shi ne rashin tsoma bakin gwamnatoci a asalin gudanar da taron da nisantar mallaka da kuma tsoma baki wajen sassautawa da tallafawa al'amura ta fuskar tabbatar da tsaro na wannan taron.

Muna ikon karbar maziyarta Arbaeen na Iran miliyan 10

Har ila yau Hujjatul Islam wal-Muslimin Sayyid Hamid Husaini, shugaban kungiyar Rediyo da Talabijin na kasar Iraki ya bayyana a cikin wannan taron cewa: Bisa la'akari da yanayin da yankin yake ciki da kuma ci gaban duniya, muna sa ran 'yan'uwa Iran mutane miliyan 10 za su halarci taron Arba'in Husaini na shekara mai zuwa a Iraki, wanda ya haifar da rashin jin daɗi ga makiya duniyar Islama da ƙarin haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu na zama abokai da 'yan'uwa. Kofar gidan mutanen Iraki a bude take ga maziyarta Sayyidush l-Shuhda (a.s.).

Har ila yau, gudanar da taron tunawa da shahidan gwagwarmaya da Gaza a farfajiyar haramin Razawi mai alfarma tare da halartar malaman Sunna da gwagwarmaya na daya daga cikin sauran shirye-shiryen taron kasa da kasa na masu fafutukar raya al'adu na Arbaeen karo na 4.