Amma dangane da lamarin kungiyar ISIS. ISIS
na nufin dukkan bam na haifar da rashin tsaro; Kungiyar ISIS tana nufin tada
zaune tsaye a Iraki, tada zaune tsaye a Siriya, da hargitsa yankin, sannan ta
zo kan babban hadafinta na karshe, wato jamhuriyar Musulunci ta Iran, don haifar
da rashin kwanciyar hankali a Jamhuriyar Musulunci ta Iran; wannan it ace babbar
manufar kuma ta karshe; Wannan shi ne ma'anar ISIS. Mun halarta; Sojojinmu sun
kasance a Iraki da Siriya saboda dalilai guda biyu: dalili na daya shi ne
"domin kare alfarma waurare masu tsarki"; Domin suna son ayi nesa da
ruhaniya da addini kuma suna da ƙiyayya da wurare masu tsarki, suna son rushe
su, kuma sun ma rushe din. Kun ga hakan a Samarra; Bayan haka, tare da taimakon
Amurkawa, sun lalata tare da tarwatsa hamuhiyar Samarra. Sun so su yin haka a
Najaf, su yi a Karbala, su yi a Kazmin, su yi a Damascus; Wannan ita ce manufar
ISIS. To, a bayyane yake; Mumini mai kishin addini mai son Ahlul Baiti ba zai
taba yin kasa agwiwa ba wajen kare irin wannan abu ba kuma ba zai kyale hakan
ya faru. Wannan dalili ne na farko.
Wani dalili kuma shine "batun tsaro". Jami'ai sun fahimci hakan da wuri kuma a kan lokaci cewa idan ba a dakatar da wannan rashin tsaro a wuraren ba, zai bazu a nan, rashin tsaro zai mamaye kasarmu mai girma. Rashin tsaro na tayar da zaune tsaye na ISIS ba abu ne na yau da kullun ba; Kowanenku ya iya tunawa da irin misalan da suka faru; A waki'ar Shahcheragh, waki'ar Kerman, waki'ar Majles da makamantansu. Duk inda suka iya, suna haifar da bala'i irin wannan. Wanda sun tsara ya rashin tsaron ya karaso nan. Amirul Muminina ya ce: Al'ummar da ta yi fada da abokan gaba a cikin gidanta, za ta wulakanta ta don haka kada ku bari sui so zuwa gidanjenku; saboda haka jami’anmu suka tafi zuwa wajen manyan zabbbun kwamandojinmu suka tafi Shahid Madaukaki agaremu Shahid Sulaimani da mataimakansa da abokan aikinsa sun tafi, matasansu suma, Duk a Iraki da Siriya - na farko a Iraki, sannan a Siriya - sun shirya da makamai, suka tsaya a gaban ISIS, sun karya bayan ISIS basu bari iya ci nasara ba. To, kasancewar mu a cikin wannan lamarin ya kasance kamar haka ne.
Ku lura da wannan gabar: nau'in kasancewar sojojinmu a kasar Siriya - irinsu a Iraki - ba yana nufin mu dauki rundunonimu, sojojinmu daa Sifah- mu kai su can ba kuma maimakon sojojin kasar ya zama sojojinmu ne ke yaki acen; A'a, bah aka abun yak e ba yin wannan ba shi da ma'ana; Wannan ba abu ne daya dace da hankali ba, haka nan kuma ra’ayin jama’a ba zai yarda cewa wata runduna ta taso daga nan za ta yi yaki maimakon sojojinsu ba; A'a, alhakin yakin yana kan sojojin kasar. Abin da sojojinmu za su iya yi, kuma suka yi, aikin bayarda shawara ne. Menene ma'anar mai ba da shawara? Yana nufin kafa muhimman sansanoni na cibiya manya, da tantance dabaru da tsara dabaru, sannan kuma idan ta kama a shiga fagen fama, amma mafi mahimmancin zaburar da matasan yankin. Tabbas matasanmu, Basijinmu su ma, sun yunkura, suna shaukin tafiya, sun dage da yawa daga cikinsu sun tafi; duk da ba mu yarda da tafiyarsu ba; Sau da yawa sun yi ta yi neman izinin tafiya, suna ta rubutowa, suna aiko saƙo, suna roƙon a bar su mu je Siriya, su tsaya a gaban abokan gaba. To, ba shakka ba’a samu dacewar hakan ba; Ma’ana bai dace ba a wancan lokacin su tafi, amma sun tafi, sun bi ta hanyoyi daban-daban – kamar yadda kuka sani; Wasu daga cikin labaransa sun shahara – wasu kuma sun yi shahada, wasu kuma sun dawo lafiya, alhamdulillahi. Babban ɓangaren aikin shine aikin shawarwari. Kasancewarmu a wurin akwai mai ba da shawara; A wasu lokuta, kasancewar sojojinmu ya zama dole, kuma galibi namu sojojin sa kai ne da na Basij [tare da] dakaru a wurin. Shahidi Sulaimani a kasar Syria ya horar, da dubban matasa sun koyi anfani da makami, suka tashi tsaye. Daga baya, ba shakka, abin takaici, wasu daga cikinsu, jami’an sojan kasar, sun koka akan hakan, suka haifar da matsaloli, kuma abin takaici sun yi watsi da wannan abin da ya dace da bukatun kansu.
Bayan da aka kashe wutar ISIS, wasu daga cikin dakarun sun dawo, wasu kuma suka tsaya; Wasu daga cikin dakarun da suka fice sun rage a can; Hakanan kuma sun kasance a irin wannan hali, amma kamar yadda na ce, ya kamata sojojin kasar ne zasu aiwatar da babban yakin. A kusa da sojojin kasar ne kuma rundunar Basij da ta fito daga wani wuri za ta iya yakin; Idan sojojin kasar suka nuna rauni, to wannan Basij din babu abin da zai iya aikatawa; Kuma abun takaici wannan shi ya faru; Lokacin da ruhun tsayin daka da gwagwarmaya ya bace, to hakan zai faru. A yau wadannan bala’o’i da ke faruwa a kasar Siriya – Allah kadai ya san tsawon lokacin da za su dauka; Har sai matasan Siriya in Allah ya yarda sun fito fili su dakatar da shi - saboda irin raunin da aka nuna a can.
Al'ummar Iran suna alfahari da sojojinsu da sojoinin Basij dinsu. Manyan jami’an soji, kungiyoyi masu dauke da makamai, a bangaren Lebanon, a bangaren Hizbullah, suna rubuto min cewa ba mu su da hakurin jure haka, ku bamu dama mu tafi; Kwatanta wannan da rundunar da ba ta da juriya da ta gudu! Abin takaici, sojojinmu sun kasance kamar haka a lokacin gwamnatin Tagut; Ba su gaba d gaba da hare-haren makiya da na kasashen waje a yaƙe-yaƙe daban-daban ba, ciki har da Yaƙin Duniya na Biyu. A wannan rana makiya sun zo su kwace Tehran da kanta; Basu tsayu ba. Yayin da basu tsayu ba kiwa, sakamakon haka zai kasance. Dole ne ku yi tsayin daka, ku yi amfani da ikon da Allah ya hore maku….