12 Disamba 2024 - 08:13
Cikakken Bayanin Jagora Ga Taron Dubban Mutane Daga Sassa Daban-Daban Dangane Canjin Yanayin Da Yankin Gabas Ta Tsakiya Ya Shiga

Da farko dai, bai kamata a yi tantama ba cewa abin da ya faru a Siriya ya samo asali ne daga wani shiri na hadin gwiwar Amurka da yahudawan sahyoniya; Na'am, akwai wata kasa da ke makwabtaka da gwamnatin Syria ta taka rawar gani a wannan fage, kuma har yanzu tana taka rawa...

بسم الله الرّحمن الرّحیم

و الحمد لله ربّ العالمین و الصّلاة و السّلام علی سیّدنا و نبیّنا ابی‌القاسم المصطفی محمّد و علی آله الاطیبین الاطهرین المنتجبین سیّما بقیّة الله فی الارضین.

Da sunan Allah, Mai rahama mai jin kai

Kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu kuma annabinmu, Abil-kasim al-Mustafi Muhammad, da iyalan gidansa salihai, tsarkaka, zababbu, musamman Baqiytullah fil Ardeen.

Ina maraba da dukkan 'yan'uwa maza da mata wadanda suka cika sararin wannan Husainiyya a yau da tsantsar soyayyarsu ta tauhidi. Musamman ’yan uwa da suka zo nan daga wasu garuruwa.

A wannan yanki namu, wanda yana daya daga cikin yankunan da suka fi daukar hankali a duniya, akwai al'amura da ke faruwa a yau; Ya kamata ayiwa waɗannan abubuwan fahimtar da ta dace, kuma a koyi darussa daga waɗannan abubuwan. Haka kuma tuninin al’ummar kasar nan ya shagaltu kan wadannan batutuwa; Suna da tambayoyi akai, suna da maganganu da suke fada, suna da ra'ayoyi akan haka; ya zama wajibi a share shubuhi dangane da hakan. Ba na nufin yin nazarin bincike kan al'amuran Siriya – binciken na wasu ne - niyyata a yau ita ce "bayyanawa da karin haske". Abin da nake nufi da “bayani” shi ne bayyana abin da ya faru wanda kuma kila a yi kokarin boye shi daga idanuwa, zamu bayani har iyaka inda muke gani kuma muke fahimta; "karin haske" [kuma] yana nufin Karin haske a cikin bayanan da zan yi yau ta hanyar nuna halin da muke ciki, motsinmu, motsin yanki, makomar yankin bisa ga fahimtarmu a cikin abubuwan da suke faruwa a yau. Kuma mu nuna wannan a matsayin sakamako da takaitaccen bayanin da zan gabatar a yau in Allah Ya yarda.

Da farko dai, bai kamata a yi tantama ba cewa abin da ya faru a Siriya ya samo asali ne daga wani shiri na hadin gwiwar Amurka da yahudawan sahyoniya; Na'am, akwai wata kasa da ke makwabtaka da gwamnatin Syria ta taka rawar gani a wannan fage, kuma har yanzu tana taka rawa - kowa na iya ganin haka - amma musabbaban asali sune dai – Amurka da Isra’ila-; mai aiwatarwa da babban mai maƙarƙashiya da babban mai shirya makirci da babban ɗakin bada umarnin yana a Amurka da gwamnatin Sahayoniya. Muna da shaidu akan haka; Waɗannan shaidun ba su barwa mutane wurin yin shakka ba.

Daya daga cikin shaidun shine yadda sukai mu’amala da wannan lamarin da ya faru. To ka gani, ace a wata ƙasa - ko da ba ku aminta da gwamnatin ƙasar ba – ya zamo yaƙi ya auku, bangarori biyu sun afkawa juna; To, wannan yana faruwa a ko'ina, amma me yasa kuke tsoma baki? A cewar labaran da ke fitowa, gwamnatin Sahayoniya ta yi ruwan bama-bamai sama da wurare 300 a Siriya! me yasa Idan ba ku da hannu a cikin wannan lamarin, idan shirin faruwar lamarin bai shafe ku ba, to ku zauna ku kuyi kallo mana. Kungiyoyi biyu suna fada da juna; Shiga cikin yaƙin ku da bombin din sama wurare ɗari uku [saboda me ne]? Amurkawa da kansu sun sanar - ba shakka, har zuwa jiya, watakila fiye da haka - cewa sun yi bombin din wurare 75! Wasu daga cikin wadannan wuraren da aka kai harin bama-bamai cibiyoyin ababen more rayuwa ne a Siriya; Akwai wuraren da ba shi da sauƙin gina shi, koxs gyara shi, kuma yana da wahala ga ƙasa ace ta iya gyarawa ko gina filin jirgin sama, gina cibiyoyin bincike, horar da masana kimiyya; Waɗannan ba ayyuka ba ne masu sauƙi. Me ya sa gwamnatin yahudawan sahyoniya da Amurka suka shiga cikin wannan harka suka zama bangare daya na yaki suka fara jefa bama-bamai a kasar? Bombin din wurare 3400 ba karamin abu bane.

Baya ga haka, gwamnatin Sahayoniya ta mamaye yankunan Siriya; Tankokinta sun isa kusa da Damashƙ. Yankin Golan da ke Damascus ta kasance a hannunsu shekaru da yawa, yanzu sun fara mamaye wasu yankuna ma. Amurka da Turai da gwamnatocin da ke kula da wadannan abubuwa a wasu kasashen duniya, suna da damuwa game mamaye mita daya ko mita goma na kasashensu, ba kawai sun yi shiru ba ne kuma ba su yi zanga-zanga akai ba, kai suna ma taimakawa ne. faruwar hakan Aikin su ne…