21 Nuwamba 2024 - 06:00
Bidiyon Yadda Isra'ila Ta Kai Mummunan Harin Sama A Kudancin Beirut

An kai wani kazamin hari ta sama a yankunan kudancin birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta bisa nakaltowa daga tashar sadarwa ta Aljazeera a safiyar yau alhamis cewa bayan fitar da sanarwar ficewa daga yankin Hare Harik da ke kudancin Dahiya, gwamnatin yahudawan sahyuniya ta kai musu hari da munanan hare-hare ta sama.

A cewar majiyoyin na Lebanon, sau 3 jirgin yaƙin gwamnatin sahyoniyawan suka kai hari a kudancin birnin Beirut a safiyar yau ɗin.