Mai ba da
shawara na jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana wa wakilan jam'iyyu da
kungiyoyin kasar Labanon cewa: Zan gaya muku sakin layi daya na sakon da
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aika zuwa ga Nabih Berri shugaban
majalisar dokokin kasar Labanon, wannan sakin layin kuwa shi ne ya ce: Dukkanin
sassan Iran sun tsaya tsayin daka wajen nuna goyon baya ga gwagwarmaya".
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya bayar da rahoton cewa, Ali Larijani mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci kuma mamba a majalisar samar da zaman lafiya ya shaidawa wakilan jam'iyyu da kungiyoyi na kasar Labanon a ranar Asabar cewa: "Na shaidawa mahukuntan Labanon cewa: taimakonmu a shirye ke, kawai ku gaya mana yada zamu aike da shi ".
Dangane da shirye-shiryen da kasar Iran ta yi na aikewa da kayan agaji zuwa kasar Labanon, ya kara da cewa: Muna cewa a aika da shi ta jirgin sama, amma kuna cewa ba zai yiwu ba. Mun ce ta a aika ta ruwa, kun ce ba zai yiwu ba, mun ce a aika kudi, kun ce an sanya wa bankunan ku takunkumi ba zai yiwu ba...
Taimakonmu ya isa ga al'ummar Lebanon a halin da ake ciki
Larijani ya kara dac cewa: Ko ta yaya, ku ba da mafita, za mu aiwatar da shi. Ko da yake ko a cikin wannan hali, taimakon da muke samu yana kaiwa ga al'ummar Lebanon.
Ya ce game da taimakon da Iran ke bayarwa don sake gina Lebanon: Wane ne ya taimaka wajen sake gina Lebanon bayan shekara ta 2006? Iran za ta sake yin hakan a lokacin da ya dace, amma a yanzu muhimmin batu shi ne tsagaita bude wuta da muka mai da hankali a kai.
Larijani ya ci gaba da cewa: Zan gaya muku sakin layi daya ne kawai na sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci da ya aike wa Barry, wannan sakon kuwa shi ne cewa: Dukkan sassan Iran sun tsaya tsayin daka wajen nuna goyon baya ga gwagwarmaya.
Kokawarsa Ga Wasu Kasashen Larabawa
Ya koka kan wasu kasashen Larabawa da suka ce a makonnin da suka gabata cewa wai an gama da Hamas, Hizbullah da Iran.
Larijani ya ce: Mun kai wa wannan gwamnatin hari da makami mai linzami har guda 200, a matsayin mayar da martani ga kazamin harin da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa yankunan kasarmu a cikin harin tabbataccen alkawari.
Ya jaddada cewa Hamas da Hizbullah da Iran sun tsaya tsayin daka kuma suna nan daram.