25 Oktoba 2024 - 17:06
Da Sadaukarwar Manyan Shahidai Irinsu Sayyid Hasan Nasrallah Da Shahid Safiyyuddin Da Shahid Haniya Da Shahid Sinwar Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Ke Zaune Lafiya

Wani bangare daga cikin hudubar sallar Juma'a na wannan mako a Brinin Alishahr, Juma'a 25 ga Nuwamba, 2024, wanda Hujjatul-Islam Wal Muslimeen Hamidinejad, limamin ya gabatar.

Ranar 8 ga watan Aban, ranar shahadar Muhammad Husain Fahmidh, kuma ranar samari, zan so in gabatar muku da wasu 'yan batutuwa gareku ababen kaunata. Aiki da ya hau kan uwa da uba ga ‘ya’yansu shine ba su tarbiya ta addini wanda idan har sukai kasa agwiwa akan kin bayar da ita garesu tom alhakin yana kansu ba zai sauka ba’ Ya rage a gare kau tunda alhakinsa a duniya da lahira yana kanku mai kyau ko marar kyau ya rage gare ku ku tsayu ga sauke wannan hakkin, na sanar da su ubangiinsu tare da taimaka masa wajen ganin yayiwa Allah ta’ala biyayya.

Kamar yadda ya zo daga Imam Sajjad As ya ce acikin littafin Risatul Hukuk: Hakkin yarnka akanka shi ne cea saboda nauyinsa yana kanku a duniya kuma zamowar  ai alkhairi da sharri gareka yake komawa ya zama wajibi ka sanar da shi Allah kuma ka taimaka masa akan biyya ga Allah.

 A yau, abin takaici, iyaye da yawa suna yin watsi da wannan muhimmin nauyi, kamar yadda Manzon Allah (saww) yake cewa, “Kaito ga ‘ya’ya a qarshen zamani daga iyayensu, domin ba sa karantar da su addini, ko da su kansu yaran suna son su koyi wani abu na addini, su na hana su”. Kuma suna ganin da zarar sun biya buqatarsu ta duniya, sai su yi zaton sun sauk hakkinsu da ke kansu.

Wasu iyaye idan suka ga 'ya'yansu suna zuwa masallaci ko karatun Alqur'ani, sai su hana su cewa maimakon masallaci da alqur'ani su tafi koyon darussan harshen turanci ko ajin kida da raye-raye!!!

An karbo daga Imam Sadik (a.s) a cikin littafin Kafi, inda ya ce: “Tun kafin a jefa karkataccen tunani ga matasa, tom ku moya musu addini”. kamar yadda zaka ji suna cewa “ tun da dai mu musulmai ai ya wadatar babu bukatar aiwatar da wasu ayyuka na addini kuma ba a bukatar yin ibada.

Yanzu a sararin samaniyar kafofin sadarwa da sada zumunta, suna ta ayyukan karkatar da tunanin da suke yada cewa: idan har zukatan matasanmu da samarinmu suka zama masu tsarki ya wadatar, ba ka bukatar su yi sallah, su sanya hijabi, ko yin azumi da sauran ibadu, alhali kuwa Annabi yana cewa mafi soyuwar halittu a wurin Allah saurayi da matashin da ya ciyar da kuruciyarsa da kyawunsa a tafarkin biyayya da bautar Allah, wanda Allah yake alfahari da shi ga  Mala'ikunsa, yana cewa da su: “Lallai wannan bawana ne na gaskiya".

Iyaye masu daraja a yau, nauyin da ke kan mu a matsayin iyaye yana da yawa, dole ne mu ceto matasan mu.

Imaminmu  Jagora Sayyid Ali Khemnae a wata ganawa da ya yi da mahalarta taron Shuhada na kasa na Kermanshah, ya yi nuni da wani muhimmin batu cewa a yau bukatar mu ga shahidai ba tai kasa da lokacin yaki ba, domin yakin yau yana hauhawa kuma ya fi wahala fiye da na Yaƙin shekaru 8 da aka kakabawa Iran. Makiyanmu a yau yana yakar mu da makamai masu zafi da makamai ruwan sanyi da tasirin al'adu.

Matasan mu a yau suna bukatar sanin irin sadaukarwa da sallamawa bisa ikhlasi da dabi'un Musulunci na matasan zamani yakin kariya mai tsarki ta yadda makiya ba za su yi tasiri a kansu ba su mayar da su dakarun tsaka-tsaki ko kuma sojojinsu.

Ya kuma ce a ranar 4 ga watan Mehr cewa matasan ta hanyar ba da ransu a lokacin yakin kariya mai tsarki  ba su bawa makiya damar daga tutarsu a kan iyakokinmu ba. A yau ba zai yiwu a’ummar kasarmu mai girma su bari ya zamo wanna tutuar an kafata a kasarmu ta hannun wasu mutane masu mukami da aka yaudare su. Kuma yayi gargadi ga ma'aikatar kimiyya da kiwon lafiya da yada labarai ta yi taka tsantsan, da alama akwai mafi yawan masu kutse a cen.

Dole ne mu gane da sanin masu tasiri kuma gaba da gaba da su kaitsaye wasun sun samu mukami mai girma wanda idan yaz amao mutane suka sansu da ganesu ba zai yi suyi aikiwa makiya ba na juyar da tunanin samarinmu.

Zamu iya ganesu sune masu cewa sanya hijabi ai zabi ne ga mata ba wajibi ba, suna cewa akan batun ‘yanto Falasdinu da Lebanon mu ba ita ce matsalarmu ba, Amurka ba makiyarmu ba ce, dangane da Amurka suna cea ba abokiyar gabanmu ba ce, suna cewa kulla alaka da Amurka zata  magance matsalar tattalin arzikinmu, kuma ma wai mutane sun gaji da gwagwarmaya, bau kamata ace mutuwa ga Amurka da Isra’ila ba, duk wadannan kalamai na masu kutse ne na makiya, ko kuma wadanda aka yaudare su, wadanda ko shakka babu al'ummar Iran suna daukarsu a matsayin makiyinsu kuma za su yi maganinsu da gaske.

A yau zaman lafiya da tsaron kasar Iran ya samu ne saboda sadaukarwar manyan shahidai irinsu Sayyid Hasan Nasrallah da Safiyyuddin da Shahid Sinwar wadanda suka dagula da hana zaman lafiyar gwamnatin sahyoniyawa tare da killace ta a wani dan karamin yanki. Idan da babu sadaukarwa wadannan masoyan na mu to da daywa daga kasashen yankin musamman Iran da yahudawan sahyoniya sun shafeta.

A yau al'ummar Iran sun fito suna taimakon al'ummar Gaza da Lebanon da ake zalunta tare da hadin kai da bada tallafin kudi, kuma ba za su gajiya ba.

 (Juma Alishahr Imamat Institution)