29 Satumba 2024 - 05:38
Salon Rayuwar Ahlul Baiti Shahada A Tafarkin Rayuwar Imam Ali (As)

Imam Ali As, ba wai kawai ba ya tsoron mutuwa, a’a ba ya ma daukar ta a matsayin abin gudu da rashin kyan gani, sai dai yana maraba da ita, kuma yana kukan cewa bai samu shahada ba.

Bayan kammala yakin Uhudu da komawar kafirai da mushrikai Makkah, sai Imam Ali, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda shi kadai ne wanda ya tabbatu wajen kare Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har zuwa lokacin karshe ya zo wajen Manzon Rahama (SAW) a cikin bacin rai da damuwa. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallama ya ce: Ali! meyasa kake bakin ciki Ali (a.s) ya ce: “Yaya ba zan yi bakin ciki ba, alhali Hamza da sauran sojoji sun samu babbar falala ta shahada, ni kuma wannan nasarar ban sameta ba.

▪️ Imam Ali As, ba wai kawai ba ya tsoron mutuwa, a’a ba ya ma daukar ta a matsayin abin gudu da rashin kyan gani, sai dai yana maraba da ita, kuma yana kukan cewa bai samu shahada ba.
Madogara: Muntahal-Amal, juzu'i na 1, shafi na 427.