18 Agusta 2024 - 08:17
Kyautatawa Ita Ce Kamshin Rayuwa Mai Kyau A Gidaje Madaukaka

Kyautatawa wani halayya ce da ake gadonta da take bin tsatso iyali daga wani zuwa wani. Idan muna tausayawa a cikin danginmu, yaranmu ma zasu koyi wannan ɗabi'ar tausayawar daga wurinmu kuma su isar da ita ga tsatso masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya maku tsokaci kan kyawawan dabi’u na zamantakewar iyali da jama’a: wanda rubuta: Muhammad Husain Amin

Wannan bayani an rubuta shi cikin yare mai sauki da harshe mai sauki da ke bayyana muhimmancin kyautatawa a cikin iyali ta fuskar Musulunci da koyarwar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su). Ta hanyar karanta wannan bayani, za ku iya koyan samun mafita mai amfani don ƙirƙirar yanayi mai dadi da abokantaka a cikin iyalinku. A cikin duniyar da lokaci ke wucewa da sauri kuma zukata sukkaraya tare da yin sanyi, dangi sukan zamo kamar mafaka mai aminci, suna ba mutane zazzafar soyayya. A cikin wannan ƙaramin mafakar, tausayi yana haskakawa kamar zinariya mai haske kuma yana bawa zamantakewa rai da rayuwa. Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) wadanda su ne mafifitan abin koyi ga bil'adama, sun jaddada muhimmancin kyautatawa da tausayawa ga iyali.

Kyautatawa umarni ne Allah:

A cikin Alkur’ani mai girma, Allah Ta’ala ya umarci muminai da su kyautata ayyukansu da kyautatawa iyalansu. A cikin suratun Nisa, aya ta 19, mun karanta cewa: “Kuma ka kyautata wa iyalanka”. Wannan aya mai daraja ta nanata muhimmancin kyawawan halaye tare da iyali a matsayin umarni na Ubangiji. Ma’ana kamar yadda yin ayyuka na addini kamar sallah da azumi suna daga cikin umarni na Ubangiji, haka nan kuma kyautata wa mata da ‘ya’yanta umarni ne daga Allah. Mutumin da yake da tsantsan ra'ayi mai tsauri a kan aiwatar da ayyukan addini da umarni na addini da hukunce-hukuncen Ubangiji, ba tare da shakka ba, zai zamo yana kula da aiwatar da wannan muhimmin umarni na da koyarwar Ubangiji.

Ruwayoyin Ahlul Baiti (Amincin Allah Ya Tabbata A Gare Su) Game Da Kyautatawa Iyali

Ahlul-baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) sun jaddada wajabcin kyautata wa mata da ‘ya’yanta a hadisai da dama. Kadan daga cikin wadannan ruwayoyin sune kamar haka:

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafi alherin ku shi ne wanda ya kyautata wa iyalansa”. (Bukhari) Imam Ali (AS): “Mafi alherin mutane su ne wadanda suke girmama manyansu da tausayawa kananansu”. (Nahjul-Balaghah) Imam Sadik (AS): "Ku kyautata wa matanku domin su kyautata muku". (Wasilish-Shia)

Wadannan ruwayoyin da suka kasance digo daga teku mara iyaka na ruwayoyin da aka samo daga Manzon Rahama (sawa) da Iyalansa (as), suna nuni da cewa kyautatawa tausaywa ba nasihar tarbiyya ce kadai ba, har ma da umarnin Ubangiji da wajibi ne kowane mumini ya bi ya aikata. Domin takaitawa, mun kawo kadan daga cikin wadannan hadisai.

Tasirin Kyautatawa Da Tausaya Ga Iyali

Kyautatawa da tausayin iyali kamar ruwa mai raya rai da rayuwa, yana ƙarfafa tushen bishiyar iyali kuma yana ba ta kwanciyar hankali. Sa’ad da dukkan iyali suka kyautatawa juna kuma suka gina ginshiƙin iyali cikin alheri, za su kasance da kwanciyar hankali da nutsuwa kuma za su iya shawo kan matsalolin rayuwa da ƙalubale cikin sauƙi. Kamar yadda itacen bishiya mai ƙarfi ya ke juriya ga iska, guguwa da sauran cututtuka fiye da ɗan ƙaramin itace.

Ƙarfafa haɗin kai na zukata da tausayawa: Tausayawa da kyautayi suna ƙarfafa haɗin kai tsakanin iyali kuma suna ƙarfafa tunanin kasancewarsu ababen dogaro da juna. Samar da yanayi mai aminci: muhallin da ya ginu bisa kyautatawa da ƙauna yana ba da yanayi mai aminci da kwanciyar hankali ga duk iyali. Girman Yaran da Nagartar Yara: Yara suna girma cikin koshin lafiya a hankali da tunani a muhallin da suke girma cikin kauna da kyautatawa. Magance husuma: tausayi da nasiha ita ce hanya mafi dacewa don magance husuma da rikicin iyali. Ƙara gamsuwar rayuwa: Iyalai masu tausayi da kyautatawa juna suna samun mafi gamsuwar rayuwa.

Kyautatawa Harshe Ne Da Kowa Ya Ke Fahimta

Kyautatawa harshe ne da ya wuce kalmomi. Kyakkyawan kallo, murmushi mai daɗi da runguma da jawowa ajika na gaske na iya kwantar da zuciyar kowane ɗan adam. A cikin iyali, kyautatawa ya kamata ta zama harshen magana da yanayi ta yadda dukan Iyalai su ji shi kuma gan shi.

Dabarun Don Ƙara Kyautatawa A Cikin Iyali

Nuna ƙauna: Ku nuna ƙauna ga iyalinku akai-akai. Sauraron dukkan bukatunsu mai ƙarfi: Ku yi saurare da kyau ga abin da iyalinku suke faɗa kuma ka fahimce su. Yabawa: Ku yaba da kyawawan halayen Iyalinku. Ku yi nishadi: Ku tsara yadda za ku ji daɗi tare. Yin sulhu cikin kwanciyar hankali: Idan jayayya ta taso, a yi ƙoƙarin warware matsalar cikin natsuwa da tattaunawa. Koyar da kyautatawa ga yara: Koya wa yaranmu kyautatawa tun suna yara kuma ka ƙarfafa su su kasance masu kirki.

Kyautatawa Gado Ne Mai Dorewa

Kyautatawa wani halayya ce da ake gadonta da take bin tsatso iyali daga wani zuwa wani. Idan muna tausayawa a cikin danginmu, yaranmu ma zasu koyi wannan ɗabi'ar tausayawar daga wurinmu kuma su isar da ita ga tsatso masu zuwa.

A ƙarshe, dole ne a ce Kyautatawa shine mabuɗin zinariya na farin cikin iyali. Ta wajen nuna tausawa da ƙauna, za mu iya zama iyali masu ƙaunar juna da son juna kuma mu zama abin koyi ga wasu.