Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da dama daga cikin mutanen kasar Iraki suna ganin gwamnatin kasar Amurka tana da hannu wajen sake farfado da kungiyar a kasar Iraki, don halattawa kanta ci gaba da wanzuwar sojojinta a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya nakalto majiyoyin tsaro na kasar Iraki runduna ta 51 na dakarun Hasdu ne suka dakile shirin mayakan na Daesh na kwace garin Makhool da ke cikin lardin Salahuddin a daren jiya laraba.
Kafin haka Jabir Almaamuri mamba a rundunar dakarun mabiya mazhabar shia a kasar ya yi gargadi kan yiyuwan gwamnatin kasar AMurka ta sake farfado da kungiyar Daesh a kasar ta Iraki, banda shiga kai tsaye da take yi a cikin harkokin siyasar kasar ta Iraki.
An kafa dakarun Hashdu ne tare da fatawar Ayatullahi Sistani a shekara ta 2014 bayan da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta mamaye wasu yankuna da dama a arewacin kasar ta Iraki. Sannan bayan da ta samu nasarar murkushe yan ta’addan, an sanya dakarun cikin jami’an tsaro na gwamnatin kasar Iraki a shekara ta 2016.
342/