10 Mayu 2022 - 15:09
Sri Lanka Na Kara Fadawa Rikicin Siyasa

Firaministan Sri lanka Mahinda Rajapaksa ya yi murabus bayan artabun da akayi tsakanin magoya bayansa da kuma masu zanga zangar adawa da gwamnatinsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Lamarin dai ya nuan yadda kasar ke kara tsunduma a rikicin siyasa da ksar bata taba ganinsa irinsa ba.

Kakakin Rajapaksa, Rohan Weliwita ya ce firaministan mai shekaru 76 ya aike da wasikar ajiye aiki zuwa ga kaninsa, shugaba Gotabaya Rajapaksa.

Hakan dai zai share fagen kafa sabuwar gwamnati a kasar dake fama da matsin tattalin arziki.

A jiya Litinin ne rikicin mafi muni ya barke a babban birnin kasar Colombo, a lokacin da magoya bayan iyalan Rajapaksa suka afka wa masu zanga zanga.

‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga zangar, kuma suka ayyana dokar ta baci a fadin kasar.

342/