27 Afirilu 2022 - 18:42
Jagora : Kyautata Alaka Da Isra’ila Da Kasashen Musulmi Ke Yi Babban Kuskure Ne

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya soki kasashen musulmi dake daidaita alakarsu da gwamnatin Isra'ila, yana mai cewa matakin wani babban kuskure ne.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gabanin ranar tunawa da masallacin Quds ta duniya da ke tafe, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayin wata ganawa da ya yi da kungiyar daliban jami'a da wakilan kungiyoyin dalibai jiya Talata a nan Tehran ya bayyana cewa "ranar Qudus ta bana za ta sha bamban da sauran da suka gabata.

Jagoran ya jinjinawa al'ummar Falastinu da ake zalunta, ya kuma ce Ranar Kudus wani lokaci ne da ya dace don nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da ake zalunta."

A daye bangaren kuma Jagoran ya soki soki yadda gwamnatin Sahayoniya take aikata munanan laifuka, kuma Amurka da Turai suna goyon bayansu”.

342/