7 Afirilu 2022 - 12:47
Kwanaki Biyar A Jere Sojojin Mamayar HKI Suna Ci Gaba Da Muzgunawa Palasdinawa A Birnin Kudus

Rahotannin da suke fitowa daga Palasdinu sun ce; kwanaki biyar kenan ajere da ‘ yan mamayar suke kai wa Palasdinawa hari a kusa da mashigar BABUL-AMUD, dake masallacin Kudus. Bugu da kari a daren jiya Laraba ‘yan mamayar sun kuma kame wasu Palasdinawa biyar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An ga sojojin na HKI sun mamaye hanyoyin da suka nufi masallacin kudus da suke unguwannin al-sahirah, sultan Sulaiman da babban titin Nablus.

Wata majiyar ta ce ‘ yan mamayar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, da kulake akan palasdinawan da kuma abubuwan fashewa masu karan gaske.

Tun da aka shiga watan nan na Ramadan mai alfarma, ‘yan sahayoniyar su ka fara kai wa palasdinawa hare-hare a masallacin Kudus.

Da akwai sojojin mamaya fiye da 200 girke a cikin birnin na Kudus zagaye da masallacin kudus mai albarka.

342/