30 Maris 2022 - 14:39
​Iran: Kulla Hulda Da Isra’ila Wasu Larabawa Ke Yi Cin Amanar Al’ummar Falastinu Ne

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi kakkausar suka kan taron da jami'an Isra'ila da Amurka da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa hudu suka yi a yankin Negev da Isra’ila ta mamaye, yana mai cewa hakan cin amanar al’ummar Falasdinu ne.

Martanin Saeed Khatibzadeh a jiya Litinin ya zo ne bayan da ministocin harkokin wajen kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Morocco, kasashen larabawa uku da suka kulla alaka da Isra’ila a shekarar 2020, gami da ministan harkokin wajen Masar, wadda dama ta jima da kulla alaka da yahudawan Isra’ila, suka hadu da jami’an Isra’ila a yankin Negev, tare da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.

Kakakin na Iran ya yi Allah wadai da wannan taro da ya kira mai muni da aka yi a yankin Falastinawa da yahudawa suka mamaye, inda ya ce yin hakan cin amanar al’umma ne baki daya.

Kakakin na Iran ya jaddada cewa ba za a 'yantar da yankunan Palastinawa da aka mamaye ba sai ta hanyar tinkarar mamayar yahudawa a Palastinu, da kuma nuna goyon bayan al'ummomin musulmi da gwamnatocin kasashen musulmi ga al’ummar Falastinu marasa kariya.

Khatibzadeh ya kammala jawabinsa da yin gargadi kan yunkurin yahudawan sahyoniya na tayar da fitina da barna a yankin.

Manyan jami'an diflomasiyya na Hadaddiyar Daular Larabawa, da Maroko, da Masar, da Bahrain, da Amurka, da kuma Isra'ila, sun kammala taro na kwanaki biyu a hamadar Negev jiya litinin da nufin ci gaba da daidaita dangantakar da ke tsakanin kasashen Larabawa da Isra’ila kamar yadda Amurka ta tsara.

Shi ma firaministan Falasdinu, Mohammad Shtayyeh a ranar Litinin din nan ya yi Allah wadai da taron da aka yi a yankin Negev da aka mamaye, yana mai cewa gudanar da irin wadannan tarurrukan yayin da Isra’ila ke ci gaba da mamayar da take yi, bata lokaci ne kawai."

342/