Shafin yanar gizo na labarai 'Afrika news' ya bayyana cewa a ranar laraban da ta gabata ce aka rantsar da Damiba a matsayin shugaban kasa na gwamnatin rikon kwarya ta shekaru uku.
Sojojin kasar Burkina Faso sun kwace mulki ne a cikin watan Jenerun da ya gabata, inda suke korafi kan tabarbarewar harkokin tsaron kasar, da wannan manufar suka ga yakamata su shiga cikin lamarin don ceton kasar.
Sabuwar gwamnatin da shugaban ya kafa a jiya dai ta kunshi ministoci 25 daga cikin har da tsohon ministan tsaro a gwamnatin da suka yiwa juyin mulki wato Janar Barthelemy Simpore.
A ranar Alhamis ce shugaban ya nada Albert Ouedraogo a matsayin shugaban gwamnati ko kuma firai ministan na gwamnatin rikon kwaryar.
342/