13 Faburairu 2022 - 13:40
FAO Na Neman $ Miliyan 130 Domin Agazawa Gabashin Afrika

Hukumar samar da abinci da raya aikin gona ta MDD (FAO), ta ce tana neman tallafin dalar Amurka miliyan 130, domin taimakawa al’ummomi dake cikin tsananin bukata, a yankunan kasashen Habasha da Kenya da Somalia, dake fama da fari.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Hukumar ta yi gargadin cewa, farin da ake ci gaba da fuskanta na haifar da karancin abinci a yankin kahon Afrika, inda mutane miliyan 12 zuwa 14 ke fuskantar barazana.

Matsalar na kara ta’azara sakamakon rashin tsirrai da ke haifar da mutuwar dabbobi.

Shugaban hukumar a yankin gabashin Afrika, David Phiri, ya ce ana bukatar kara daukar matakai a yanzu, domin kaucewa shiga matsalar jin kai.

342/