Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa a cikin kwanaki biyu da ya yi a tarayyar Nageriya shugaban kasar Turkiyya ya bude cibiyar raya al’adu ta kasar Turkiyya a birnin Abuja, sannan an sanya hannu a kan yarjeniyoyi daban-daban har guda 8 tsakanin kasashen biyu.
Banda haka shugaba Erdogan ya gana da yan kasuwan Najeriya karkashin kwamitin kasuwancin tsakanin kasashen biyu. A na shi bangaren shugaba Buhari ya yabawa shugaba Erdogan da shirinsa na daukar nauyin yan gudun hijira miliyon 4 daga kasashen Siriya, Afganistan da Iraki.
342/