Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Premium times ta Najeriya ta ce, ta ga wasikar wacce aka rubuta da harshen hausa, dauke da sunayen duk wadanda suke garkuwa da su, wacce kuma ‘yan bindigan suka bawa daya daga cikin wadanda suke garkuwa da su don isar da ita ga sarkin.
Kafin haka dai ‘yan bindigan sun kai farmaki kan wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni inda suka kashe jami’an tsaro 21 da garuruwan Dama da kuma Gangara, sai kuma mutane 20 a Gatawa, sannan suka kama wasu suka yi awon gaba da su.
Kananan hukumomin Isa da Sabon Birni na daga cikin kananan hukumomi 14 wadanda ake katse wayoyin tarho a cikinsu don magance matsalar ‘yan bindigan.
342/