Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shugaba Raisi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar tarkardun kama aiki daga sabon jakadan Burtaniya a Tehran Simon Shercliff a jiya Lahadi.
Ya ce bisa dabi’ar mutanen Iran, a duk lokacin da suka ji cewa wasu kasashe na cin zarafinsu, to sukan kara turjiya da kuma kin mika wuya, inda ya ce, 'yancin kai da kuma yanci na ‘yan adamtaka su ne manyan taken mutanen Iran.
Haka nan kuma shugaban na Iran ya kara da cewa, za su yi mu’amala da kasashen duniya ne a bisa wannan asasi, ta yadda babu wanda zai cutu idan aka kiyaye hakan.
Sannan ya bayyana cewa, kasar Burtaniya wadda take da tsohuwar alaka da Iran, kasashen biyu za su iya yin aiki tare a bangarori daban-daban domin ci gaban al’ummominsu, amma bisa girmama juna.
342/