Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shugaban ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko ga taron babban zauren MDD karo 76 da ke gudana a birnin New York na kasar Amurka a jiya Talata.
Sayyid Ra’isi ya kara da cewa abubuwa guda biyu sun zama tarihi na rashin nasara ga Amurka a baya –bayan nan, na farko shi ne aukawar mutanen A murka cikin majalisar dokokin kasar Amurka a ranar 6 ga watan Jeneru na wannan shekarar da kuma ficewar Amurka daga kasar Afganistan ba tare da shiri ba.
Dangane da shirin Iran na makamashin Nukliya na zaman lafiya kuma, Sayyid Ra’isi ya bayyana cewa ba wanda yake bin Iran bashi a aiwatar da yarjejeniyar JCPOA don Iran har yanzun ta na cikin yarjejeniyar, Amurka ce ta fice daga cikinta, don haka dole ne Amurka ta amince ta daukewa kasar Iran dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar, kafin Iran ta koma kan alkawuranta na JCPOA.
342/