ABNA24 : Za’a dai gudanar da bikin ne a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan Jagoran, kamar yadda ofishin Jagoran ya sanar ranar Lahadi.
Bikin zai samu halartar wasu daga cikin manyan jami’an kasar, inda ministan cikin gida zai gabatar da rahoto kan zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yunin da ya gbata.
An tsara kuma jagoran Imam Khamenei da zababben shugaban kasar zasuyi jawabi a gun bikin na yau Talata.
A ranar Alhamis ne, kuma zababben shugaban kasar ta Iran Ibrahim Ra’isin zai yi rantsuwar kama aiki a hukumance.
An bayyana cewa baki 115 ne daga kasashen duniya 73 zasu halarci bikin rantsar da zababben shugaban kasar Ebrahim Raïssi, wanda zai gaji shugaba Hassan Rohani wanda ke kan kammala wa’adin mulkinsa na biyu kuma na karshe.
342/