ABNA24 : Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 92 sanadiyyar gobarar, a yayinda wasu 110 kuma suka samu kuna masu tsanani a jikinsu.
Har’ila yau labarin ya kara da cewa mai yuwa a kara samun karin gawawwaki a cikin burbushin asbitin da ya kona .
Shugaban hukumar kare hakkin fararen hula ta kasar Iraqi ya bayyana cewa babu isassun kayakin yaki da gobara a asbitin wanda yakamata ace shuwagabannin asbitin sun samar da su a asabin Imam Husain (a) da ke garin na Ziqar na lardin Nasiriya daga kudancin kasar.
Wasu labaran sun bayyana cewa an fadawa hukumomin asbitan kan cewa iskar gas na tsiyayewa a asbitin kafin aukuwar gobarar.
342/